Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru sun yi kira da a karfafa hadin gwiwa game da yaki da ta'addanci
2020-09-25 19:57:08        cri

Masana da suka halarci taron karawa juna sani game da yaki da ta'addanci, da sauya tunanin masu tsattsauran ra'ayi, da kare hakkin bil Adama da ya gudana a kamon jiya, sun yi kira ga sassan kasa da kasa, da su karfafa hadin gwiwa da juna, don cimma nasarar da aka sanya gaba.

Taron na kwararru, wanda ya gudana a ranar 17 ga watan Satumba, ya samar da dandali ga mahalartan sa, na tattauna karin muhimman batutuwa da suka hada da zakulo dabarun yaki da ayyukan ta'addanci tsakanin kasa da kasa, da sauya tunanin masu tsattsauran ra'ayi, da muyasa a wadannan fannoni.

Da yake tsokaci yayin taron, wakilin dindindin na Sin a ofishin MDD dake Geneva na kasar Switzerland, da sauran hukumomin kasa da kasa dake ofishin Chen Xu, ya ce tun farkon wannan shekara, bullar cutar COVID-19 ya haifar da sabbin hadurran da kalubaloli ga yakin da duniya ke yi da ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Chen Xu ya ce akwai bukatar sassan kasa da kasa su kafa tsarin hadin kai, don cimma kafuwar al'ummar duniya mai makoma guda, su kuma shiga a dama da su wajen aiwatar da manufofin MDD masu nasaba da yaki da ta'addanci, da yayata manufofin cudanyar sassa daban daban, da hadin gwiwar kasa da kasa.

Kaza lika a cewarsa, ya dace kasashen duniya su karfafa ikon juna na cimma nasarori a wadannan fannoni, musamman ma kasashe masu tasowa, ta yadda za su iya shawo kan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, tare da kara bunkasawa, da kuma kare hakkokin bil Adama.

Sauran kwararru na Sin da kasashen waje da suka halarci wannan taro, sun gabatar da shawarar aiwatar da matakan kasa da kasa na bunkasa yaki da ta'addanci, suna masu fatan kasashe mambobin MDD za su karfafa hadin gwiwa da tsare tsare, tare da musayar managartan dabarun shawo kan ta'addanci a matakin kasa da kasa.

Ofishin zaunannen wakilan kasar Sin dake MDD a birnin Geneva, da tawagar wakilan sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, da ofishin wakilin dindindin na kasar Kamaru a MDD dake Geneva, da wasu hukumomin kasa da kasa dake kasar Switzerland, da kuma cibiyar nazarin dabarun kare hakkin bil Adama ta kasar Sin ne suka shirya wannan taro cikin hadin gwiwa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China