![]() |
|
2020-09-25 11:20:02 cri |
A yayin bikin, Mr. Zhang Lijun ya ce, ambaliyar ruwa da ta afka wa jamhuriyar Nijer a watanni shida a karshen wannan shekara, ta kuma haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi a kasar. Lamarin da ya sa nan da nan ofishin jakadancin kasar Sin ya amsa kirar gwamnatin Nijer, inda ta tara kudade don taimakawa al'ummar Nijer da ambaliya ta shafa. Jakadan ya jaddada cewa, a daidai lokacin da kasashen duniya ke fuskantar kalubaloli na annobar COVID-19 da bala'u daga indallahi da kuma karancin abinci, ya zama dole kasashen duniya su hada kansu. Ya kuma yi imani da cewa, bisa matakan da gwamnatin Nijer da al'ummarta suka dauka da ma taimako da sassa daban daban suka samar, Nijer za ta warware matsalar da ke gabanta.
A nasa bangaren, Mr. Magagi Laouan ya yi nuni da cewa, shekaru hudu a jere ke nan ofishin jakadancin kasar Sin ke samar da gudummawar kudi ga jama'ar Nijer da ambaliya ta shafa, matakin da ya kara shaida cewa, kasar Sin babbar kawar Jamhuriyar Nijer ce. A madadin shugaba Mahamadou Issoufou da gwamnatinsa da kuma jama'ar kasar Nijar, ministan ya mika godiya ga kasar Sin, ya kuma gaskata cewa, hadin gwiwar kasashen biyu zai kawo karin alheri ga Nijer.(Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China