Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aminu Wali: Sin ta taka muhimmiyar rawa a ci gaban tattalin arzikin Nijeriya
2020-09-25 11:17:23        cri

A ranar 23 ga wata, tsohon ministan harkokin wajen Nijeriya, kana tsohon jakadan kasar a kasar Sin, Aminu Wali ya tattauna tare da wakilin kafar yada labarai ta Premium Times, dangane da batun rancen kudin da kasar Sin ta baiwa Najeriya da ma matsalar ciniki a tsakanin Sin da Amurka.

A yayin tattaunawar, Aminu Wali ya ce, a matsayinmu, ba wai muna sayar da kanmu ga kasar Sin ba ne, a'a, haka kuma ita kasar Sin ba ta taba kwace albarkatun kasarmu ba. Kasar Sin tana fatan shiga a dama da ita a aikin bunkasa Nijeriya, kuma a shirye take ta samar da gudummawarta gwargwadon bukatar Nijeriya, musamman ta fannin bunkasa manyan ababen more rayuwa. Matsalar bashi, ba Nijeriya ce take fuskanta ba, batu ne da ya zama ruwan dare har ma a Turai da sauran sassan duniya. Bisa tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ne kasar Sin take samar da rancen kudi ga kasashen Afirka, ciki har da Nijeriya, rancen da muke biyan dan kudin ruwa kadan, kuma duk wani shugaba mai hankali na kasarmu ba zai yi fatali da rawar da kasar Sin ke takawa wajen bunkasa tattalin arzikinmu ba, don haka, ya kamata Nijeriya ta ci gaba da hulda da kasar Sin.

Aminu Wali ya ci gaba da cewa, bai kamata kasashen Afirka su tsoma baki cikin matsalar ciniki a tsakanin Sin da Amurka ba. Ci gaban kasar Sin ya sa Amurka ta daina zama mai fada a ji ita kadai a duniya, sai dai hakan ya bakanta mata rai. Matsalar ciniki a tsakanin kasashen biyu ba matsalarmu ba ce, ballantana ma suke ta kokarin gano bakin zaren warware matsalar.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China