Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jama'ar Qinghai sun kyautata rayuwarsu ta hanyar dogaro da fasanar samar da wutar lantarki ta amfani da haske rana
2020-09-21 16:36:13        cri

Lardin Qinghai yana kan babban tsaunin Qingzang, wurin dake da fifiko wajen samar da wutar lantarki ta amfani da haske rana, a shekarun baya-baya nan, lardin Qinghai ya bullo da wasu muhimman sassa, kamar masana da kimiyya da kudade da dai sauransu, don kafa masana'anta, matakin da ya taimaka wajen kyautata tattalin arziki da hallitu da ma rayuwar jama'a.

A karshen shekarar 2018, an kashe kudin Sin RMB Yuan miliyan 344 don kafa tashar samar da wutar lantarki ta amfani da haske rana a yankin Talatan, ruwan da aka yi amfani da shi domin wanke na'urorin lokaci-lokaci, ya taimakawa tsirrai. Wang Yucheng ya shafe fiye da shekaru 20 yana kiwon raguna a wurin, ya koma wannan wuri a shekarar bara saboda yadda filin ciyawa ya farfado.

Wannan tashar ba kyautata muhallin hallitu take yi ba kawai, kuma kashi 60 cikin dari na kudin shigarta, an zuba su cikin sha'ani daban-daban a wurin, tare da samar da guraben aikin yi ga mazauna kewayen, sauran kashi 40 cikin 100 ana amfani da su don biyan albashin kauyawa. Wadda ke zaune a wurin mai suna Liu Yonglian ta fara aiki a kamfanin sarrafa abinci da aka kafa ba da dadewa ba a garin, ana biyanta albashi ne daga kudin da aka samu daga wannan tashar karkashin shirin kawar da talauci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China