Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da wasanni a babbar ganuwa domin murnar bikin kwanaki 500 suka rage a gudanar da wasannin Olympic na Beijing 2022
2020-09-21 13:43:11        cri

A ranar Lahadi an gudanar da wasanni a babbar ganuwar kasar Sin dake dutsen Badaling, a gundumar Yanqing na birnin Beijing, domin yin maraba da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu, wato Beijing 2022 Olympic wanda ya rage kwanaki 500 a gudanar.

'Yan wasa daga dukkan fadin kasar Sin an basu damar nuna ayyukan takardun da suka yanka. A daren Lahadi, an kuma shirya bikin kide-kide na yayata gasar ta Beijing 2022.

Aikin yanka takardu da babbar ganuwa su ne alamomin al'adun gargajiya na birnin Zhangjiakou da na yankin Yanqing na birnin Beijing da za su gudanar da gasar a shekarar 2022.

He Jianghai, mataimakin sakataren kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ya ce, kasancewar kwanaki 500 ne suka rage a gudanar da gasar babban cigaba ne. Yace yana fata wasannin gargajiyar da aka gabatar a daren Lahadi zasu kara yayata gasar ta Beijing 2022 Olympic Winter Games ga dukkan mutanen kasar Sin.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China