Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a bude gidajen sinima da na motsa jiki a Ikko
2020-09-20 15:31:31        cri
Jahar Ikko, cibiyar kasuwancin Najeriya za ta sake bude gidajen sinima da wuraren motsa jiki bayan shafe watanni suna rufe sakamakon bullar annobar COVID-19.

Gwamnan jahar Ikko Babajide Sanwo-Olu, ya tabbatarwa kafafen yada labaru a ranar Asabar cewa, an baiwa masu gidajen sinima da wuraren motsa jiki a jahar goron albishir na sake budewa nan bada jimawa ba matukar dai sun kiyaye bin dukkan matakan kariya da suka dace.

Sai dai kuma, gwamnan ya ce, bude gidajen sinimar da wuraren motsa jikin za a baiwa mahalarta kashi daya bisa uku na yawan adadin mutanen da cibiyoyin suke iya dauka ne, wanda hakan yana daga cikin yarjejeniyoyin da aka cimma da jami'an dake gudanar da al'amurran cibiyoyin.

Sanwo-Olu ya ce, an kuma baiwa coci-coci da masallatai izinin gudanar da cikakken ayyukan ibadu, sai dai tilas ne su kiyaye daukar dukkan matakan kariya.

Gwamnan na Ikko ya kara da cewa, gidajen sayar da barasa, da gidajen rawa, da cibiyoyin shirya taruka, za su cigaba da kasancewa a rufe har sai abin da hali ya yi. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China