Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kiyaye zaman lafiyar duniya shine burin bai daya na dukkan bil Adam
2020-09-19 18:24:04        cri

Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 75 da kafuwar MDD, kana shekara ce ta cika shekaru 30 da sojojin kasar Sin suka shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. A cikin shekaru 30 da suka gabata, Sin ta kara nuna goyon baya ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, wadda ta kasance muhimmin jigo a ayyukan. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun mayar da aikin kiyaye zaman lafiyar duniya a matsayin wani muhimmin nauyin dake bisa wuyansu.

A watan Afrilun shekarar 1990, sojojin kasar Sin sun tura masu sa ido kan aikin soja guda 5 zuwa kungiyar sa ido ga tsagaita bude wuta ta MDD, ta hakan sojojin Sin sun fara shiga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. A shekarar 2009, Sin ta zama kasar da ta fi tura sojojin kiyaye zaman lafiya a cikin kasashe 5 na kasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD. Ban da aikin sa ido kan tsagaita bude wuta, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sun bada tabbaci ga manyan ayyuka da jigilar kayayyaki da kuma ayyukan likitanci na MDD, hakan sun samar da goyon baya ga tawagogin musamman na kiyaye zaman lafiya na MDD, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen sake gina kasar da suke gudanar da ayyukan da kyautata zaman rayuwar kasar baki daya.

A sabon zamani, an fadada sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin daga sojojin ma'aikata da jigila da likitanci zuwa sojojin kasa da jiragen sama. Kana an kara ayyukansu kamar taimakawa kiyaye zaman lafiya, da bada kariya ga fararen hula, da kiyaye tsaro da dai sauransu, haka kuma sun samar da babbar gudummawa wajen magance rikice-rikice, da daidaita matsaloli, da tabbatar da tsaron fararen hula da ma'aikatan tawagogin musamman na MDD da kuma ayyukan more rayuwa da sauransu.

Shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da sojojin kasar Sin ke yi ya sa kaimi ga hada kan bangarori daban daban na duniya wajen kiyaye zaman lafiya tare da tabbatar da tsaro yayin da ake kokarin samun bunkasuwa tare a zamantakewar al'ummar 'yan Adam baki daya. Shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da sojojin kasar Sin ke yi ya shaida cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD, da bin ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa wajen tabbatar da ra'ayin bangarori daban daban, da adalci, da more zaman lafiya, da kuma sa kaimi ga shimfida zaman lafiya da samun wadata tare.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, sojojin kasar Sin sun shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD sau 25, yawan sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura ya kai fiye da dubu 40. Sojojin kasar Sin sun kasance wani muhimmin bangare wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, da kuma tabbatar da zaman lafiyar duniya. Kiyaye zaman lafiyar duniya shine burin bai daya na dukkan bil Adam. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China