Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da takardar bayani game da gudummawar sojojin Sin a aikin wanzar da zaman lafiya na MDD
2020-09-18 11:34:35        cri

A Yau Juma'a ne ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani, game da gudummawar sojojin Sin a aikin wanzar da zaman lafiya na MDD. An dai yi wa takardar lakabi da "Dakarun sojin Sin: shekaru 30 cikin aikin wanzar da zaman lafiya na MDD."

Takardar bayanin ta fayyace yadda gudummawar sojojin Sin a ayyukan MDD, ta zamo jigo ga ayyukan majalissar shekaru 30 da suka gabata. Ta ce dakarun wanzar da zaman lafiya na Sin sun kafa tarihi a kasashe da yankuna sama da 20, ciki hadda Cambodia, da Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Liberia, da Sudan. Sauran sun hada da Lebanon, da Cyprus, da Sudan ta Kudu, da Mali da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Wadannan tawagogi dai sun ba da gudummawa, wajen warware rikice rikice da wanzar da zaman lafiya, da kafa ginshikin tsaro da daidaito a yankuna, tare da habaka ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar da ke kasashen da ake gudanar da ayyukan. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China