Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da takardar bayanai game da batun ayyukan yi da hakkin 'yan kwadago a Xinjiang
2020-09-17 11:30:52        cri
A jiya Alhamis ne kasar Sin, ta fitar da takardar bayani game da batutuwan da suka shafi ayyukan yi, da hakkokin 'yan kwadago a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin.

Takardar wadda ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin ya fitar, ta ce Xinjiang na daukar batun samar da guraben ayyukan yi a matsayin wani muhimmin ginshiki, na inganta rayuwar al'umma.

Takardar bayanin mai taken "Ayyukan yi da hakkokin kwadago a Xinjiang, ta ce karkashin tsarin kyautata ayyuka da ka'idojin kwadago, Xinjiang na ci gaba da kyautata rayuwar mutane a fannonin samar da wadata da raya al'adu. haka lika jihar na tabbatar da kare hakkokin bil Adama a fannoni da dama.

Takaradar bayanin dai na kunshe ne da babuka shida, wadanda suka hada da batun ayyukan yi a Xinjiang, da ka'idojin kwadago masu muhimmanci, da batun kare martaba da zabin ma'aikata, da hakkokin kwadago. Sauran sun hada da samar da managartan ayyukan yi don kyautata rayuwar jama'a, da aiwatar da ka'idojin kwadago da na kare hakkokin bil Adama na kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China