Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Madam Peng Liyuan ta yi kira ga mata da su taka rawar gani wajen yaki da talauci
2020-09-16 13:37:42        cri

Yau Laraba 16 ga wata a nan birnin Beijing, an yi taron bita dangane da yadda ake yaki da kangin talauci a karni na 21 da muke ciki, da kuma rawar da mata suke takawa a wannan fanni, inda uwar gidan shugaban kasar Sin Xi Jinping madam Peng Liyuan, ta yi jawabi ta kafar bidiyo.

A cikin jawabinta, madam Peng Liyuan ta ce, kasar Sin na himmantuwa wajen fitar da mata masu fama da talauci daga fatara. Ta ce ana daukar matakai da dama a fannonin raya tattalin arziki, da samar da guraben aikin yi, da habaka ciniki, da ba da ilmi, da ba da tabbacin zaman rayuwa, da kiwon lafiya da dai sauransu, wadanda suka samu kyawawan sakamako.

A cikin mutane fiye da miliyan 700 da aka fitar da su daga kangin talauci, rabinsu mata ne. Mata masu dimbin yawa a kasar Sin sun amsa kiran gwamnatin kasar na yaki da fatara cikin himma da kwazo, sun kuma taka muhimmiyar rawarsu a matsayin ginshikai na yaki da talauci kamar yadda maza suke yi.

Madam Peng ta kuma yi kira ga sassa daban daban na kasa da kasa, da su hada gwiwa, su dauki matakai don ilmantar da mata yadda ya kamata, da ba su zarafin samun aikin yi kamar yadda ake baiwa maza, a kokarin raya sha'anin mata, da sha'anin tattalin arziki tare. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China