Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nacewa kan manufofi hudu zai ingiza hulda tsakanin Sin da Turai
2020-09-15 21:07:49        cri

A yammacin jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar karba karba ta kungiyar EU kuma shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Dorothea Merkel, da shugaban kungiyar kasashen Turai Charles Michel, da shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen ta kafar bidiyo, inda ya jaddada cewa, ya kamata a nace kan manufofi hudu wato zaman tare cikin lumana, da gudanar da hadin gwiwa ba tare da rufa rufa ba, da gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, da kuma daidaita harkokin kasa da kasa ta hanyar yin tattaunawa, hakika shawarar da shugaba Xi ya gabatar za ta jagoranci ci gaban huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai a nan gaba.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, idan Sin da Turai suna zaman tare cikin lumana, to za a kara shimfida zaman lafiya da wadata a fadin duniya, tsokacinsa ya sake nanata babbar ma'anar ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Turai, yanzu, wasu 'yan siyasar kasashen yamma suna da makarkashiyar tayar da tarzoma a cikin harkokin kasa da kasa, inda suke son tayar da yakin cacar baka, lamarin da zai kawo barazana ga tsaron duniya, a bisa wannan yanayi, ya kamata Sin da Turai su kara fahimta cewa, babu sabani mai tsanani a tsakaninsu, gudanar da hadin gwiwa ya fi yin takara kyau.

A halin yanzu tattalin arzikin duniya da cinikayyar kasa da kasa sun gamu da babbar matsala sakamakon bazuwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, amma kasar Sin da kasashen Turai suna ci gaba da gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu, ko shakka babu suna taimakawa farfadowar tattalin arzikin duniya matuka.

Kana manufar habaka cudanyar tattalin arziki a kasuwannin cikin gida da na ketare da kasar Sin take aiwatarwa tana samar da sabbin damammaki ga kasashen Turai.

Yayin ganawarsu a jiya, sassan biyu sun daddale yarjejeniyar kyautata muhalli, sun kuma tabbatar da cewa, za su hanzarta yin tattaunawa kan zuba jari, duk wadannan za su kara habaka hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da kasashen Turai, su ma kamfanonin kasashen Turai dake gudanar da harkokinsu a nan kasar Sin sun bayyana cewa, suna cike da imanin saboda Sin da Turai suna kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China