Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farfadowar tattalin arzikin Sin tana ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya
2020-09-15 21:00:56        cri

Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar yau sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu karuwa a watan Agustan da ya gabata, duk da cewa, tana fama da tasirin yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 da bala'in ambaliyar ruwa, lamarin da zai ingiza cudanyar tattalin arziki a kasuwannin cikin gida da na ketare, shi ma yana ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya.

Ingiza cudanya a kasuwannin cikin gidan kasar Sin yana nufin ya dace a kara habaka bukatun cikin gida, sabbin alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, kasar Sin tana da wannan karfin, saboda tana da cikakken tsarin masana'antu da fifikon babbar kasuwa da kuma karfin kirkire-kirkire a asirce.

Hakika a watan Agustan da ya wuce, karuwar ayyukan masana'antun kasar Sin ta kai kaso 5.6 bisa dari idan aka kwatanta da makamacin lokacin bara, adadin da ya fi na watan Yuli yawa har zuwa kaso 0.8 bisa dari, kana alkaluman aikin ba da hidima ya karu da kaso 4 bisa dari, adadin da ya fi na watan Yuli da kaso 0.5 bisa dari, ban da haka, kwatankwacin adadin kayayyakin da aka sayar a watan Agusta ya karu da kaso 0.5 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, wannan shi ne karo na farko da ya karu a cikin shekarar bana, haka kuma yanayin sayayya da zuba jari a kasar ta Sin yana kara kyautatuwa, jaridar The Wall Street Journal ta wallafa wani rahoto, dake bayyana cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu ya fi hasashen da aka yi.

An lura cewa, a watan Agusta, karuwar cinikayya da jarin waje ita ma ta fi hasashen da aka yi yawa, wato adadin shige da fice na watan ya karu da kaso 6 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, a sa'i daya kuma, adadin jarin wajen da aka yi amfani da su a watan Agusta ya karu da kaso 18.7 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, duk wadannan sun aza harsashe mai inganci ga habakar tattalin arziki a kasuwannin cikin gida da na ketare.

An samu wadannan nasarori, saboda matakan gwamnatin kasar Sin na kara bude kofa ga ketare, misali manyan bukukuwa uku wato bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin, da wadanda ake fitarwa daga kasar da aka fi sani da "Canton Fair", da bikin baje kolin cinikayyar ba da hidimomi, da bikin baje kolin CIIE da aka gudanar suna taka babbar rawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Nan gaba kuma tattalin arzikin kasar Sin zai kara farfadowa, saboda habakar bukatun cikin gida da karuwar zuba jari da ta sayayya, shi ma zai ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya,(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China