Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin ministan harkokin wajen Sin: ya kamata a koyi darasi daga lamarin "9.11", da zurfafa hadin kan kasa da kasa na yaki da COVID-19
2020-09-14 16:45:16        cri
A kwanan baya ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Luo Zhaohui, a madadin wakilin majalisar gudanarwar kasar, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi wanda har yanzu ke ziyarar aiki a ketare, ya halarci taron ministocin harkokin waje ta kafar bidiyo, na dandalin tattaunawar yankin ASEAN (ARF) karo na 27, inda ya nuna yabo sosai kan kokarin da ARF ya yi cikin dogon lokaci, game da daukar matakan da suka dace, da kiyaye zaman lafiya da zaman karko na yankin, kana ya jaddada cewa, ya kamata a koyi darasi daga harin ta'addanci da ya faru a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001, a kuma zurfafa hadin kai a tsakanin kasa da kasa, wajen yaki da annobar numfashi ta COVID-19. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China