Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Somalia: An kaddamar da layin waya na ko-ta-kwana domin agazawa hidimar kiwon lafiya
2020-09-14 13:54:38        cri
Kungiyar ba da agajin jin kai na Red Crescent dake aiki a Somalia ko SRCS a takaice, ta kaddamar da lambar waya 446, domin baiwa al'ummar birnin damar kira, a duk lokacin da suka fuskanci wani yanayi na gaggawa mai alaka da ceton rayuka.

An dai kaddamar da lambar ne a birnin Mogadishu, inda ake sa ran jama'a za su amfana da wannan tsari dare da rana, don samun tallafin farko na kula da lafiya, da kuma hidimar sufurin masu bukatar kulawa ta gaggawa.

Wata sanarwa da jami'i mai jagorantar kungiyar na birnin Mogadishu Nur Abdikarim Ali ya fitar a jiya Lahadi, ta ce motocin SRCS za su rika daukar marasa lafiya kyauta, kuma masu aikin sa kai na kungiyar ne ke gudanar da aiki da su.

Ali ya kara da cewa, manufar samar da lambar wayar, shi ne ceton rayukan al'umma. Kuma lambar wayar za ta rika saduwa ne da masu gudanar da aikin tallafin, wato ma'aikatan jinya, da mai amsar sakon, da jagoran tawagar masu aikin.

Fatan dai a cewar Mr. Ali, shi ne sabuwar lambar da aka kaddamar, ta samar da karin damar kyautatawa, da inganta ayyukan kiwon lafiya na gaggawa a birnin Mogadishu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China