Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda ake yin amfani da filin hamada wajen gudanar da aikin noma a yammacin kasar Sin
2020-09-14 12:11:15        cri

Wasu wuraren dake arewa maso yammacin kasar Sin, su kan gamu da matsalar fari, inda rashin ruwa ke hana ci gaban tattalin arziki. Sai dai a garin Jiuquan dake lardin Gansu, an fara daukar fasahar noma a cikin hamada.

A cikin wani gandun noma dake karkarar garin Jiuquan, ana ganin jerin manyan rumfunan noma, wadanda a cikinsu manoma suke kokarin kula da kayan lambu da 'ya'yan itatuwan da za su nuna.

"A cikin wannan rumfa, an dasa gurji. Wanda aka dasa a ranekun 3 da 4 ga watan Agusta. Ana sa ran za su nuna zuwa ranar 10 ga watan Satumba. Gaba daya za a bukaci kwanaki 35 zuwa 40."

Bayan da Qin Cunguo ya shiga cikin rumfar nomansa, ya fara gabatar da kayan lambun da ya shuka a ciki. A matsayin wani manomi, Qin ya dade yana kokarin kula da gonakinsa da fadinsu ya kai hekta 2, kuma bai taba tsammanin cewa wata rana zai zama mutum da ya fara samun wadata a cikin kauyensa ba.

A shekarar 2018, Qin ya ji yadda hukumar kauyensa ke shirin kafa rumfuna a cikin hamada, don noman kayan lambu. Ya yi tunani sosai, daga bisani ya yi hayar fili daga wajen kungiyar hadin kan manoma dake kauyensa, inda ya fara aikin noman kayan lambu da rumfar noma.

"Da ma ni da matata muna kula da gonakinmu hekta 2. Ba ma samun kudi sosai, ba sa isar mu zaman rayuwar yau da kullum. Don haka muka kafa wadannan rumfuna. Da farko dai muna da damuwa kan wasu abubuwa. Amma aikin sai an mai da hankali a kansa sosai. Mai nema yana tare da samu."

Saboda a da bai taba kula da rumfar noma ba, shi ya sa ya tafi wajen wasu kwararrun da suka san fasahohin noma na zamani, ya yi kokarin koyon fasahohi. Ba da dadewa ba, ya fara kwarewa sosai a fannonin zabar iri, da kawar da kwari, da sarrafa na'urorin dake cikin rumfar noma, da dai sauransu. A bara, tumatir da ya yi nomansa cikin rumfuna guda 2 ya samu karbuwa sosai a kasuwa. Ganin haka ya sa shi neman habaka tsarin aikinsa, inda ya yi hayar karin wasu rumfuna 3 a bana, don noman tumatir da kokamba.

"A rumfa guda za a iya samun kudin Sin Yuan dubu 40. In an cire kudin da na zuba, riba tsantsa za ta kai dubu 30 zuwa dubu 35." A cewar Qin, kudin da ya samu a rumfa daya ya zama daidai da ribar da ya samu daga gonakinsa hekta 2. Hakan ya karfafa gwiwarsa sosai, inda yake neman mai da cikakken hankalinsa kan aikin noma a cikin rumfuna.

"Na yi shirin ci gaba da habaka aikina na noma a cikin rumfa. Zan saurari ra'ayi na kwararru, don zabar nau'ikan kayan lambu masu kyau, da samar da kayayyaki masu matukar inganci. Hakan zai taimakawa biyan bukatun mutanen garinmu na cin abinci, har ma akwai damar sayar da kayayyakin da na samar zuwa wurare daban daban na kasar mu, don biyan bukatun jama'ar kasarmu."

Rumfunan Qin suna cikin wani gandun noma na musamman, inda ya riga ya janyo hankalin kamfanoni fiye da 20, da kungiyoyin manoma, domin su yi hadin gwiwa wajen kafa rumfuna 2500. Kana kayan lambun da ake samar da su daga cikin rumfunan, kai tsaye ana jigilarsu zuwa cikin kasuwannin wasu manyan birane, irinsu Beijing, da Shanghai, da Guangzhou. A cewar Madam Wu Haixia, wata jami'a mai kula da wannan aiki, ana kokarin kafa wani tsarin da zai amfani kowa. Ta ce,

"Mun yi amfani da wani tsarin da ya shafi hadin gwiwar kamfanoni, da kungiyoyin manoma, da cibiyar samar da kayan lambu, ta yadda kamfanoni za su samu damar habaka ayyukansu, kana manoma su ma za su more sakamakon da aka samu, ta hanyar raya aikin gona na zamani cikin yankin hamada." (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China