Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gibin kasafin kudin Amurka a farkon watanni 11 na 2020 ya kai dala triliyan 3
2020-09-13 16:27:20        cri

A ranar 11 ga wata, hukumar kula da baitulmalin kasar Amurka ta fitar da wani rahoto, inda aka bayyana cewa, a farkon watanni 11 na shekarar kudi ta 2020 wato tsakanin ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2019 zuwa ranar 30 ga watan Satumban shekarar 2020, gibin kasafin kudin kasar ya riga ya kai dala triliyan 3, adadin ya zarce gibin shekarar kudin ta 2009 matuka, inda aka yi fama da rikicin kudi mafi tsanani.

Rahoton shi ma ya bayyana cewa, gibin kasafin kudin kasar na watan Agustan da ya gabata ya kai dala biliyan 200, adadin da ya yi daidai da na makamancin lokacin bara.

Kana ofishin kasafin kudin majalisar dokokin Amurka ya yi hasashen cewa, saboda barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, kudin shigar gwamnatin kasar ya ragu, kuma kudin da ta kashe ya karu, a sanadin haka, gibin kasafin kudin shekarar kudi ta 2020 na kasar zai kai dala triliyan 3.3, adadin da zai ninki har sau uku idan an kwatanta da na shekarar 2019, kana gibin kasafin kudin zai kai kaso 16 bisa dari na adadin GDPn kasar, kuma adadin zai kai matsayin koli tun bayan shekarar 1945, ban da haka kuma, adadin bashin gwamnatin kasar a shekarar kudi ta 2021 zai zarta GDPn kasar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China