Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe ta yabawa kasar Sin bisa tallafin da take samar mata a fannin dakile cutar COVID-19
2020-09-11 15:11:09        cri


Ministar yada labarai ta kasar Zimbabwe Monica Mutsvangwa, ta fadawa wakilin CMG a wajen intabiyun da aka yi mata cewa, kasarta ta godewa kasar Sin bisa tallafin da take samar mata a kokarin dakile cutar COVID-19.

Monica Mutsvangwa, ita ce ministar kasar Zimbabwe, mai kula da aikin yada labarai. Ta fadawa wakilin CMG cewa, yadda kasar Sin ta samu nasarar shawo kan yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri ya burge ta matuka, don haka tana son taya mutanen kasar Sin murna kan wannan babbar nasarar da suka samu. Ban da wannan kuma, ta ce tana godiya sosai ga gwamnatin Sin, saboda kasar ta yi iyakacin kokarinta don taimakawa sauran kasashe, ciki har da kasar ta Zimbabwe, ko da yake ita ma tana fuskantar matsin lamba sosai yayin da take kokarin dakile annobar. Ministar ta ce,

"Tun bayan da aka samu barkewar cutar numfashi ta COVID-19, gwamnatin kasar Sin, da kungiyoyin jama'ar kasar, sun samar da kayayyakin da ake tsananin bukatarsu ga kasar Zimbabwe. A nasa bangaren, ofishin jakadancin kasar Sin dake Zimbabwe a kusan kowane mako yana samar da kayayyakin kandagarki ga kasar Zimbabwe a matsayin kyauta, lamarin da ya taimaka matuka ga kokarin inganta kayayyakin kandagarkin da likitocin kasar Zimbabwe suke amfani da su. An ce da abokin daka ake shan gari. Ma iya cewa a ko da yaushe kasar Sin tana tare da mu."

Ban da wannan kuma, Madam Mutsvangwa, ta ambaci yadda kasar Sin ta tura tawagogin likitoci zuwa kasar Zimbabwe, domin taimakawa kasar a fannin fasahar kandagarkin cutar. A cewar ta,

"Annobar COVID-19 ta janyo babban kabubale ga kasashe daban daban. Saboda haka, muna tsananin bukatar koyon fasahohin zamani na sauran kasashe, a kokarinmu na tinkarar cutar. Gaskiya gwamnatin kasar Zimbabwe da jama'ar kasar suna matukar godiya, kan yadda gwamnatin kasar Sin ta turo mana tawagar likitoci, don ba da taimako ga aikin dakile cutar. Kwararrun likitocin kasar Sin sun bayyana mana dukkan dabarun kandagarkin cutar COVID-19, da fasahohin da aka samu a fannin jinyar masu kamuwar da cutar. Sa'an nan wadannan fasahohi da dabaru na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa a kokarinmu na ganin bayan cutar COVID-19. "

Tun a watan Mayun bana, hukumar lafiya ta kasar Sin ta bukaci a zabi wasu kwararrun likitoci daga lardin Hunan dake tsakiyar kasar, don tura su zuwa kasar Zimbabwe, inda suka yi aiki kafada da kafada da abokan aikinsu na kasar Zimbabwe, don taimakawa aikin dakile yaduwar annobar. Wadannan likitocin kasar Sin su 12, sun yi kwanaki 14 suna gudanar da ayyukansu a kasar Zimbabwe, inda suka raba fasahohinsu na tinkarar cutar COVID-19 tare da likitocin kasar Zimbabwe. Ta wannan hanya, sun taimaki kasar Zimbabwe sosai, a kokarinsu na dakile annobar.

A cewar minista Mutsvangwa, albarkacin goyon bayan da kasar Sin ta baiwa Zimbabwe, da sauran matakan da kasar Zimbabwe ta dauka wajen dakile cutar, yanzu an samu saukin yaduwar cutar COVID-19 a kasar Zimbabwe, kana tattalin arzikin kasar yana samun farfadowa. Ministar ta kara da cewa ,

"Cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar da babbar illa ga zaman rayuwarmu, ta kuma gurgunta tattalin arzikin kasar Zimbabwe sosai. Duk da haka, wani abin da nake so na jaddada shi ne, mun riga mun samu shawo kan yaduwar cutar, bisa taimakon da aminiyarmu, wato kasar Sin, ta ba mu."

Ban da wannan kuma, ministar yada labaran ta kasar Zimbabwe, Monica Mutsvangwa, ta bayyana fatanta na ganin kasashen Zimbabwe da Sin za su iya zurfafa hadin gwiwarsu, a fannonin gwaje-gwajen allurar rigakafin cutar COVID-19, da yin amfani da ita, da musayar fasahohin tinkarar cutar, da dai makamantansu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China