Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta karrama wadanda suka taka rawa a yakin da kasar ta yi da COVID-19
2020-09-09 14:39:36        cri

A jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karrama wadanda suka bayar da gagarumar gudummawa, a yakin da kasar ta yi da annobar COVID-19, inda aka ba su lambar yabo ta Jamhuriya da karramawa ta kasa.

Kadan daga cikin wadanda suka lashe wadannan lambobi, sun hada da, masanin cututtukan hanyar numfashi, Zhong Nanshan da masanin magungunan gargajiya da na zamani Zhang Boli, da shugaban asibitin jinyar masu fama da COVID-19 dake Wuhan Zhang Dingyu, sai kuma Madam Chen Wei mai bincike a fannin samar da alluran riga kafin COVID-19 da sauran magungunan kariya.

Baya ga masana harkar lafiya, akwai kuma daidaikun jama'a da kungiyoyi, da mambobin JKS da kungiyoyi masu zaman kansu da sauransu da su ma aka karrama da irin wadannan lambobi daban-daban.

Yanzu dai Sin ta sake taka rawar gani a yakin da bil-Adama ke yi da cututtuka, da kishin da 'yan kasa baki daya suka nuna, da sadaukarwa, da mutunta shawarwarin kimiya da mutunta daukacin bil-Adama.

Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya jaddada, cewar nuna son kai, da dorawa wasu laifi, da jirkita gaskiya da karya, ba kawai za su illata kasa da al'ummarta ba, amma za su illata al'ummomin duniya baki daya. A don haka ya bukaci, da a kara zage damtse, don ganin bayan wannan annoba. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China