Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin sanyawa kamfanin SMIC takunkumi nuna karfin tuwo ne in ji ma'aikatar harkokin wajen Sin
2020-09-07 21:32:50        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai na yau Litinin cewa, tunanin da Amurka ke yi na sanyawa kamfanin SMIC na Sin tarnaki kuskure ne, kuma bangare ne na matakan da Amurkan ke aiwatarwa, ta hanyar fakewa da tsaron kasa don muzgunawa kamfanonin ketare.

Zhao Lijian ya ce a baya bayan nan, Amurka na amfani da batun tsaron kasa, tana amfani da karfin mulki wajen cusgunawa kamfanin kasar Sin dake hada hada a yankunan ta, ba tare da gabatar da wasu sahihan shaidu ba.

Jami'in ya ce, hakan nuna karfin tuwo ne da Sin ba za ta taba amincewa da shi ba. Bugu da kari a cewar Mr. Zhao, Amurka ta gurgunta tsarin kasuwanci mai nagarta, ta lalata salon takara mai tsafta. Ya ce baya ga keta ka'idojin cinikayya na kasa da kasa, a hannu guda, Amurkan ta kuma illata tsarin samar da hajojin masana'antu, da cinikayyar su, tare da haifar da koma baya ga moriyar ita kan ta Amurkan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China