Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi karin haske game da batun sabunta takardun ba da damar aiki ta 'yan jaridar Amurka
2020-09-07 20:34:11        cri
Sabanin zargin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya yi, cewa ma'aikatar harkokin wajen Sin ta sanar da bangaren Amurka, cewa ba za ta tsawaita wa'adin takardun shaidar ba da damar aikin wasu 'yan jarida na Amurka dake aiki a Sin ba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Zhao Lijian, ya ce wannan sanarwa da bangaren Amurka ta fitar ba gaskiya ba ce.

Zhao wanda ya kore wannan zargi, yayin taron manema labarai da ya gudana a Litinin din nan, ya ce ma'aikatar harkokin wajen Sin, na duba takardun 'yan jaridar da ke neman tsawaita damar aikin su a kasar Sin, ciki hadda masu aiki da kafar CNN, kuma yayin da ake ci gaba da wannan aiki, ba wani abu da zai shafi fannonin aiki da rayuwar 'yan jaridar. Kaza lika, tuni Sin ta shaidawa bangaren Amurka hakan. (SAMINU)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China