Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko me ya sa kasuwannin hada-hadar kudin kasar Sin ke iya jawo hankalin jarin kasashen waje daban-daban
2020-09-07 20:30:04        cri

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa, na kasar Sin na shekarar 2020 a nan birnin Beijing, kuma hukumomin hada-hadar kudi 43 daga kasashe ko yankuna 18 sun halarci taron baje kolin hada-hadar ba da hidimar kudi, wadanda suka hada da Morgan Stanley, da UBS Securities, da bankin Jamus da dai sauransu. Dukkaninsu dai sun nuna himma da gwazo wajen shiga bikin, da ma bayyana niyyarsu ga makomar bunkasuwar kasuwannin hada-hadar kudi ta kasar Sin.

Dalilin amincewar su ga kasuwannin hada-hadar kudin kasar Sin, shi ne karfin tinkarar mawuyancin hali, da tattalin arzikin a manyan fannoni da Sin ke da shi. Jaridar Economist ta Birtaniya ta ce, Sin ta samarwa cibiyoyi masu jarin ketare karuwar jimillar GDP, wadda sauran kasashe ba za su iya samarwa ba, da ma nagataccen yanayin tattalin arziki.

A sa'i daya kuma, Sin ta gabatar da wasu matakan bude kofa ga ketare ta fuskar hada-hadar kudi a shekarun baya bayan nan. A tsawon rabin shekara da ya gabata, bankunan zuba jari na kasashen ketare, da ma bankunan harkokin kasuwanci na ketare, sun shiga kasuwar kasar Sin bi da bi.

Kwalejin nazarin tattalin arziki na PIIE, ya ba da wani rahoto kwanan baya cewa, yawan kudin dake shafar kasuwar hada-hadar ba da hidimar kudi ya kai dalar Amurka triliyan 47. Idan hukumomi masu jarin waje sun kai ga kara zuba jari a Sin, to za su samu dimbin riba. A hakika dai, hukumomin na kasar Amurka suna shiga wannan aiki, abin da ya nuna cewa, katse huldar hada-hadar kudi tsakanin Sin da Amurka ba zai yiwu ba.

Ban da wannan kuma, tsarin da Sin take kafawa na hadin kanta da kasashen waje ta fuskar hada-hadar kudi, mai kunshe da bude kofarta ga ketare, zai zama wani mataki da ya fi jawo hankalin jarin waje. Kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin mai matukar bude kofarta ga ketare, za ta yi hadin kai da kasashen ketare ta fuskar hada-hadar kudi, ta yadda kamfanoni masu samar da kayayyaki, za su ci gajiya, da ma amfanar da tsarin tattalin arziki gaba daya na samun moriya da ci gajiya tare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China