Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
China CIFTIS 2020: Akwai yiwuwar manufofin Sin za su kyautata makomar tattalin arzikin duniya
2020-09-07 16:29:06        cri

Masu hikimar magana suna cewa, Juma'a mai kyau tun daga Laraba ake gane ta. Ko shakka babu, alamu sun nuna akwai yiwuwar tsare tsare da manufofin tattalin arzikin da kasar Sin ke ci gaba da bullowa da su za su iya yin babban tasiri ga ci gaban harkokin ciniki da ma tattalin arzikin duniya. Ga masu bibbiyar al'amurran dake wakana game da sha'anin tattalin arzikin duniya, ana sane da cewa, a ranar 4 ga wannan watan na Satumba ne aka kaddamar da taron bajekolin ayyukan hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020, wato "China CIFTIS 2020" a takaice. A lokacin bude taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi ta kafar bidiyo, kuma jawabin shugaban yana kunshe da batutuwa da dama, musamman wasu muhimman shawarwari game da hadin gwiwa a fannin hada hadar ayyukan hidima, inda ya sanar da kudurin kasar Sin na yin hadin gwiwa da kasa da kasa kan batun hada hada a fannin ayyukan hidimar. Bugu da kari, shugaban ya jaddada aniyar kasar Sin na zurfafa manufar bude kofarta ga ketare. Ko shakka babu, wannan mataki zai kara ingiza samun tabbaci da karfin samun bunkasuwar ci gaban tattalin arzikin duniya gami da cudanyar kasuwanci tsakanin kasa da kasa.

Kasancewar wannan ne babban taron ciniki da tattalin arziki na kasa da kasa irinsa na farko da aka gudanar a kasar Sin ta kafar intanet da ma na zahiri tun bayan barkewar annobar COVID-19, taron bajekolin ayyukan hidimomin ya ja hankalin kamfanoni da cibiyoyi daga kasashen duniya da shiyyoyi sama da 148, kana sama da mahalarta 190,000 ne suka yi rijistar shiga taron. Koda yake, a yanzu duniya na fuskantar rashin tabbas game da makomar tattalin arziki, sai dai wani abin faranta rai shi ne, a cikin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya furta wasu kalamai masu cike da karfafa gwiwar kasa da kasa game da makomar tattalin arzikin duniya, shugaban ya zayyana hanyoyin da za su zama mafita ga duniya. Ya yi nuni da cewa, kara bude kofa, da yin hadin gwiwa a fannonin samar da hidima ga jama'a wani muhimmin mataki ne na samun ci gaba. Sannan ya tabo batun hadin gwiwa mai dacewa, inda ya yi kira ga dukkan kasashen duniya su yi aiki tare, don ingiza hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkre, haka kuma kasashe su yi aiki tare, don bullo da wani sabon yanayi na hadin gwiwar moriyar juna.

Gyara kayanka dai ba zai taba zama sauke mu raba ba, har kullum kasar Sin tana daukar kwararan matakan kara bude kofarta ga tsarin tattalin arzikin duniya, kuma tana ci gaba da nacewa kan manufarta na karfafa hadin gwiwa da al'ummar duniya, da goyon bayan ra'ayin hadin gwiwar bangarori daban danan, sannan a hannu guda tana adawa da ra'ayin kashin kai da babakere, da nuna kariyar ciniki. A koda yaushe, burin kasar Sin shi ne a gudu tare a tsira tare domin samar da kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama. Hakika, wadannan manufofi na kasar Sin za su samar da makoma mai haske wajen bunkasa harkokin cinikayyar kasa da kasa da kyautata makomar tattalin arzikin duniya baki. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China