Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Sin: Tallafin da Sin ke samarwa Afirka a fannin kandagarkin COVID-19 zai ingiza ci gaban hulda tsakanin sassan biyu
2020-09-07 11:10:00        cri


A ranar 5 ga wata, agogon wurin, tawagar masanan kiwon lafiyar kasar Sin da ta kunshi likitoci takwas sun tashi daga Conakry, fadar mulkin kasar Guinea domin dawowa kasar ta Sin, bayan da suka kammala aikinsu na kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen Sudan ta Kudu da Guinea. Kafin tashinsu, shugaban tawagar Liang Chaozhao ya zanta da wakilinmu na CMG, inda ya bayyana cewa, tallafin da kasar Sin take samarwa kasashen Afirka a bangaren dakile annobar zai ingiza ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Afirka.

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ce ta kafa tawagar masanan kiwon lafiyar domin samar da taimako ga Sudan ta Kudu da kuma Guinea yayin da suke kokarin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, hukumar kiwon lafiya ta lardin Anhui ce ta zabi wadannan likitoci takwas, wadanda suka fito daga sassan likitanci daban daban, misali sashen cutar da ake samu ta harbuwa da kwayar cutar, da sashen cuta mai yaduwa, da sashen cutar numfashi, da sashen cuta mai tsanani, da sashen tantance ilmin likitanci, da sashen nas nas, wadannan masanan kiwon lafiyar kasar Sin sun gudanar da aikin kandagarkin cutar COVID-19 a Sudan ta Kudu tsakanin ranakun 19 zuwa 27 ga watan Agusta, daga baya sun ci gaba da aiki a Guinea daga ranar 27 ga watan Agusta har zuwa ranar 4 ga wannan wata.

Shugaban tawagar kuma shugaban asibitin koyarwa na jami'ar likitancin Anhui na farko Liang Chaozhao ya bayyana cewa, sun gudanar da aikin tallafawa wajen dakile cutar a Sudan ta Kudu da Guinea ne domin tabbatar da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin taron kolin musamman da kasashen Sin da Afirka suka kira domin gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu a bangaren kandagarkin cutar COVID-19, sun kuma samu maraba da tarba matuka daga bangarori daban daban na kasashen biyu. Yana mai cewa, "Yayin da muke aiki a Sudan da Kudu da Guinea, mun yi bincike da nazari kan hukumomin kasashen da abin ya shafa, misali asibiti da dakin gwaji da kasuwa da sauransu, daga baya mun gabatar da wasu shawarwari ga ma'aikatan kiwon laifya na kasashen biyu, muna fatan za su ga bayan cutar cikin hanzari. Kana mun lura cewa, gwamnatoci da al'ummu da kuma ma'aikatan kiwon lafiya na wadannan kasashen biyu sun mai da hankali sosai kan aikinmu, hakazalika, sun nuna mana godiya da goyon baya, kuma daukacinmu mun ji dadin zumunci da amincin da suka nuna mana."

Farfesa Liang ya kara da cewa, yayin da suke aiki a Sudan ta Kudu da kuma Guinea, sun ga yadda ci gaban kasar Sin ya burge al'ummun kasashen, kana ma'aikatan kiwon lafiyar kasashen su ma sun baiwa takwarorinsu na kasar Sin goyon baya da kuma tallafin da suke bukata, wani lokaci ma, su kan gaida su da yaren Sinanci, yana mai cewa, "Ya kamata mu more fasahohinmu na kandagarkin cutar COVID-19 da al'ummun kasashen Afirka, har ma da daukacin al'ummun kasa da kasa baki daya, ta haka za mu iya ganin bayan kwayar cutar a fadin duniya, saboda kwayar cuta ba ta san iyakar kasa ba, kuma babu bambanci tsakanin kabilu daban daban wajen harbuwa da kwayar cutar. Hakika bayan da muka isa nahiyar Afirka, mun kara fahimta cewa, mu ba manzannin lafiya kawai ba ne, mu manzannin sada zumunta ne, abun farin ciki shi ne, ci gaban kasar Sin da ci gaban da kasar Sin ta samu wajen fasahohin likitanci, musammam matakan da kasar Sin ta dauka a fannin dakile annobar COVID-19 sun taimaka wa al'ummun kasashen Afirka matuka. Ban da haka, yayin da likitocin sassan biyu suke yin cudanya, likitocin Sudan ta Kudu da Guinea su ma sun amince da rawar da kasar Sin take takawa kan ci gaban duniya, musamman ma a bangaren yaki da cutar COVID-19."

Farfesa Liang ya ci gaba da cewa, ko shakka babu kokarin da kasar Sin take wajen samar da tallafin kandagarkin cutar ga kasashen Afirka zai ingiza ci gaban huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka, a cewarsa: "Bayan da muka raba fasahohin dakile cutar da Sudan ta Kudu da Guinea, tabbas kasashen biyu da sauran kasashen Afirka, za su dakile annobar cikin sauri, haka kuma za su dawo da ayyuka da harkokin kiwon lafiya da zaman rayuwa yadda ya kamata. A don haka ina ganin cewa, mun zo kasashen ne ba domin samar da tallafin kandagarkin cutar kawai ba ne, muna fatan kokarinmu zai ingiza ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Afirka da hadin gwiwar sana'o'i daban daban dake tsakanin sassan biyu."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China