2020-09-05 17:41:37 cri |
A cewar mista Marube, kasar Sin daya ce daga cikin manyan abokan huldar kasar Kenya ta fuskar ciniki, sa'an nan kasar Kenya tana dora muhimmanci sosai ga aikin sayar da kayayyaki a kasuwar kasar Sin. A ganinsa, damar halartar bikin cinikayyar hidimomi a wannan karo ta sanya kasar Kenya kara lura da ciniki a wannan fanni, wadda kuma ke samar da cikakkun damammakin hadin gwiwa ga kamfanoni masu kula da ayyukan jinya, da sadarwa, da jigilar kaya, da bankuna, da inshora, da makamantansu. Ta la'akari da yadda annobar COVID-19 ke haifar da tsaiko ga kasuwanci da cinikin kasa da kasa, hada hadar ayyukan bada hadimomi zai iya taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya, musamman ma bayan da aka samu shawo kan cutar, in ji jami'in na kasar Kenya. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China