Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sassaucin Da Hukumar Kula Da Shige Da Ficen Nijeriya Ta Yi A Kan Biza Ga 'Yan Kasashen Waje
2020-09-05 16:21:07        cri

A kokarinta na share hawayen matafiya kasashen waje daga Nijeriya da kuma baki 'yan kasashen waje da ke shige da ficen kasar nan da suka makale saboda cutar Korona, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta dauki matakin mayar da tsarin bayar da biza-nan-take da takardar izinin aiki na wucin-gadi ga baki zuwa shafin intanet.

Wannan yana daga cikin matakan da hukumar ta dauka a yayin da ta karbi bakuncin masu ruwa da tsaki sama da 100 a wani taro da ta gudanar ta hoton bidiyo a shafin intanet domin tattauna batutuwan da suka haifar da damuwa sakamakon cutar Korona.

Har ila yau, a taron wanda ya gudana a Larabar da ta gabata, an lalubo bakin zaren magance matsalolin da suka shafi zaman baki a kasa da shigowarsu daga waje sakamakon rufe tashoshin jiragen sama.

Ministan cikin gida, Rauf Ogbeni Aregbesola ya samu wakilcin Daraktan sha'anin hakkokin kasa da kasuwanci, Mista Stephen Okon a wurin taron, kana mai bai wa shugaban kasa shawara a kan masana'antu da kasuwanci da zuba jari, Dakta Jumoke Oduwole ita ma ta halarci taron ta hoton bidiyo.

NIS ta dauki matakin mayar da tsarin bayar da biza-nan-take da takardar izinin aiki na wucin-gadi ga baki ne a kokarin da take yi na inganta ayyukanta ga al'umma da kuma bin turbar kudirin gwamnati mai ci yanzu na saukaka matakan hada-hadar kasuwanci.

Da yake gabatar da jawabi ga mahalarta taron, Shugaban NIS, Muhammad Babandede MFR, ya bayyana cewa a halin yanzu masu neman biza-nan-take za su iya gabatar da bukatarsu ta shafin intanet, su biya kudi ta nan sannan su samu izinin ta nan.

Ya kara da cewa, an mayar da tsarin bayar da takardar izinin aiki na wucin-gadi ga baki ta shafin intanet ne domin kawar da jami'ai masu-shiga-tsakani, inda hakan yake saba wa yin komai cin gaskiya da kawo cikas ga kokarin saukaka matakan hada-hadar kasuwanci. Wakazalika, hukumar ta dauki matakin ne domin cimma muradin Kwamitin Shugaban Kasa A Kan Samar da Kyakkyawan Yanayin Kasuwanci (PEBEC) kamar yadda yake kunshe a tsarin kwamitin na 'NAP 5.0' a game da shige da ficen mutane.

Har ila yau, Babandede ya ce mayar da lamarin zuwa shafin intanet zai rage wa masu nema irin kudin da suke kashewa na sufuri da karin kudin da ma'aikatan da ke nema musu takardun izinin suke cajinsu saboda kai-komon da suke yi zuwa Abuja domin samar musu da ko dai biza-nan-take ko kuma izinin aiki na wucin-gadi.

Ya ce a yau dai an kawo karshen kashe-kashen kudin da ba su wajaba ba da samun tsaiko na ba-gaira-ba-dalili da ake cin karo da su yayin neman takardun izinin, yana mai jaddada cewa NIS ta sha damarar kawar da duk wani abu da zai zama kadangaren bakin-tulu ga kokarin saukaka matakan kasuwanci a cikin kasa ta hanyar mayar da tsarin takardun biza-nan-take da izinin aiki na wucin-gadi zuwa shafin intanet baki daya.

A sakamakon haka, CGI Babandede ya ba da umurnin kebe adireshin email sukutum: twp@immigration.gov.ng domin gabatar da bukatar neman takardar izinin aiki na wucin-gadi ga baki a cikin Nijeriya.

Bugu da kari, NIS ta ce wajibi ne a nemi bizar aiki a cikin Nijeriya a ofisoshin jakadancin kasar da ke waje amma ba a cikin kasa ba. Kundin tsarin biza na Nijeriya na shekarar 2020 ya yi cikakken bayani a kan ire-iren biza da wuraren da ake karbar su. Biza-nan-take ta kasu kashi biyu, akwai ta 'Yan Afirka wadda ake bayarwa a mashigin kasa da kuma ta kasuwanci wacce ake gabatar da bukatarta ta intanet, a biya ta intanet kuma a samu sahalewarta ta nan.

Hukumar tana kara tunatar da jama'a cewa babu fa batun kara wa'adi ga wanda bizarsa ta aiki na wucin-gadi ta gama aiki ko ga mai biza ta takaitaccen lokaci sai fa in akwai wasu abubuwa na musamman da suka kunno kai, nan ma dole sai shugaban NIS ya amince.

Bayan haka, a taron, NIS ta dauki karin wasu matakai dangane da abubuwan da suka shafi takardun izinin shige da ficen Nijeriya domin saukaka wa baki na ciki da wajen kasa saboda matsalar Korona, kasancewar Gwamnatin Tarayya ta amince a ci gaba da sufurin jiragen sama zuwa kasashen waje a filin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas da kuma na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a ranar 5 ga Satumban 2020.

Matakan wanda aka tsara su bisa la'akari da umurnin da Ministan Cikin Gida Aregbesola ya bayar a cikin watan Afirilun 2020 na sauwake biyan kudin biza saboda cutar Korona sun hada da: tsawaita izini ba tare da biyan ko kwabo ba ga bakin da takardunsu suka gama aiki daga ranar 23 ga Maris zuwa 5 ga Satumban 2020, wadanda suke da shaidun tikitin komawa na jirgi, domin ba su damar ficewa kafin ko a ranar 15 ga Satumban 2020.

Haka nan, dukkan bakin da takardun izininsu suka gama aiki kafin 23 ga Maris da ya gabata, za su biya tara ta adadin kwanakin da suka kara kafin rufe kasa a dai ranar ta 23 ga Maris din. Mataki na gaba shi ne dukkan bakin da suke zaune a kasa wadanda tafiya ta kai su waje sai takardunsu suka gama aiki a can daga 23 ga Maris ta 2020, za a bar su su dawo cikin kasa da takardun a ranar 25 ga Satumban 2020 ko kafin nan. Sai dai za su sabunta izininsu a tsakanin kwana 30 da dawowarsu ko su fuskanci hukuncin dokar shige da fice.

Wakazalika, NIS ta amince wa dukkan bakin da suka nemi biza-nan-take da sauran nau'o'in biza daga ofisoshin jakadancin Nijeriya kafin ranar 23 ga Maris ta 2020, su gabatar da bukatar a sabunta musu ta hanyar shigar da kwafen shaidar biyan kudinsu a wannan adireshin na intanet: cis-evisa@immigration.gov.ng kafin ranar 15 ga Satumban 2020.

Haka nan hukumar ta sahale wa dukkan bakin da suka samu wasikun da ake aikewa kafin samun amincewar za a ba su biza ta kowane nau'i daga ofisoshin jakadancin Nijeriya, kafin 23 ga Maris ta 2020, wadanda har ila yau takardar amincewarsu ko bizarsu ta gama aiki kafin 5 ga Satumban 2020, su ma su gabatar da bukatar a sabunta musu ta hanyar shigar da takardun nasu da suka gama aiki a wannan adireshin na intanet: cis-evisa@immigration.gov.ng ba tare da biyan sabon kudi ba, akalla kafin nan da ranar 15 ga Satumban 2020.

A wata takarda da Jami'in hulda da jama'a na NIS, DCI Sunday James ya aike wa LEADERSHIP A Yau, hukumar ta kuma ayyana bude shafukan intanet na neman biza-nan-take da sauran nau'o'in biza ta intanet domin biyan kudi da kuma bai wa baki masu niyyar shigowa Nijeriya damar fara nema daga ranar 5 ga Satumban 2020.

Takardar ta kara da cewa, idan kuma aka samu akasi, ofishin da baki suka karbi takardar amincewa a ba su izinin aiki na wucin-gadi ko ofishin jakadancin da za su karbi bizar yana rufe, su gabatar da korafinsu ta wannan adireshin na intanet: cis-evisa@immigration.gov.ng

Haka nan, sanarwar ta ce sashenta da ke filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, zai fara bayar da takardun biza kamar yadda aka tsara a kundin bizar Nijeriya na 2020, da zarar an bude filayen jirgin guda biyu.

NIS dai ta yi gargadin cewa duk wanda ya taka doka ko ya saba ka'idar da aka bayar zai fuskanci hukunci. Kana ta ce Shugabanta CGI Muhammad Babandede ya amince a rika gudanar da irin wannan taron tare da masu ruwa da tsaki duk bayan wata uku. (Daga Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China