Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban Sin sun koma makaranta sakamakon matakan kandagarkin COVID-19 da gwamnatin kasar ta dauka
2020-09-04 10:44:47        cri

Tun daga farkon watan Satumban da muke ciki, daukacin daliban kasar Sin sun koma makaranta domin ci gaba da darussa. Gwamnatin kasar ta tsai da kudurin bude makaranta daga duk fannoni a fadin kasar ne saboda an riga an cimma nasarar hana yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a dukkan sassan kasar baki daya, kuma abun faranta rai shi ne, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, babu sabon rahoton wani ko wasu da suka harbu da cutar a daukacin jihohi, ko yankuna, ko birane dake fadin kasar ta Sin.

Duk da cewa, daliban kasar Sin ba su daina yin karatu yayin da ake kokarin kandagarkin annobar ba, wato dukkanin daliban makarantun firamare, da na makarantun midil, da na jami'o'i, dukkansu suna ci gaba da karatunsu a gida ta hanyar yin amfani da yanar gizo.

Kaza lika an bude wasu makarantu a wasu sassan kasar, inda ake zaton suna iya tabbatar da lafiyar dalibai kafin 'yan watannin da suka gabata, amma yawancin sassan kasar ba su bude makaranta ba sai yanzu, musamman ma jami'o'i, inda dalibai ke taruwa bayan dawowa daga gidajensu dake sassa daban daban na fadin kasar, kuma ana ganin jami'o'in ba za su cimma sharadun tabbatar da tsaron lafiyar dalibai da ake bukata ba tukuna. Amma a yanzu kasar Sin ta riga ta samu babban sakamako a bangaren hana yaduwar annobar, shi ya sa a kwanakin baya bayan nan, ma'aikatar kula da aikin ba da ilmi ta kasar ta sanar da cewa, lokaci ya yi da za a bude makaranta daga duk fannoni a kasar.

Amma a halin yanzu, ana ci gaba da fama da rikicin bazuwar annobar, saboda ba a iya hana yaduwarta a sauran sassan duniya ba. Misali a kasar Amurka, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya riga ya kai sama da miliyan 6, kana ya zuwa karshen jiya Alhamis, bisa jimilla, adadin wadanda suka harbu da cutar COVID-19 a dukkanin sassan duniya, ya kai mutane 26,141,903, ciki hadda mutane 861,899 da cutar ta hallaka.

A karkashin irin wannan yanayi, ya zama dole al'ummun Sinawa su ci gaba da daukar matakan kandagarkin cutar a ko da yaushe, saboda hakan ba wai zai iya tabbatar da tsaron rayukan dalilan dake karatu a cikin makarantun sassan kasar ba ne kadai, har ma zai tabbatar da tsaron daukacin al'ummun kasar baki daya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China