Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin kimiyar Sin ya samu lambar yabo ta kirkire-kirkire da nazari da ba da ilmi daga APEC
2020-09-03 11:24:52        cri

An gabatar da sakamakon zaben wadanda suka lashe lambar yabo ta kirkire-kirkire, da nazari, da ba da ilmi na kungiyar raya tattalin arzikin yankin Asiya-Pacific wato APEC ta shekarar 2020 a jiya Laraba, inda masanin kimiya daga kasar Sin Chen Huai, daga kwalejin nazarin hallitu dake birnin Chengdu, na cibiyar kimiya da fasaha ta kasar Sin, ya samu wannan lamba, bisa nazarin da yake yi a fannin hallitu iri daban-daban a fadama da dai sauransu.

A cikin wata sanarwar da APEC ta fitar, an ce fadama na iya shigo da iskar cabon dioxide, lamarin da ke iya kyautata muhalli, da ma dakile sauyin yanayi a duniya.

Lambar da aka bayar a wannan karo na da taken "Hallitu iri daban-daban masu taimakawa wajen raya tattalin arziki mai wadata".

Babban sakataren sashin kimiya da fasaha da kirkire-kirkire na kasar Malaysia Siti Hamisah ya ce, nazarin da Chenhuai ya yi, ya bayyana hakikanin ma'anar wannan take a bana, duba da cewa hallitu iri daban-daban na da muhimmanci sosai ga APEC, masu mambobin dake da albarkatu daga indallahi masu dimbin yawa, kuma kara ilmi a wannan fanni zai tamaka, wajen tinkarar kalubaloli, da ma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikinta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China