Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi kira da nacewa manufar martaba juna yayin tafiyar da harkokin kasashen duniya
2020-09-02 11:17:16        cri

A jiya Talata ne a nan birnin Beijing, aka kira taron kara wa juna sani na kasa da kasa, mai taken "kara karfafa manufar gudanar da harkokin kasashen duniya tsakanin bangarori daban daban, don kago makoma mai kyau", albarkacin ranar cika shekaru 75 da kafuwar MDD.

Mahalarta taron sun bayyana cewa, abu mafi muhimmanci a halin yanzu shi ne, nacewa ka'idojin MDD, da kuma nacewa manufar martaba juna yayin da ake tafiyar da harkokin kasashen duniya, wadda hakan ce hanya daya kacal, ta kyautata rayuwar bil Adama.

Tun bayan da aka kafa MDD kafin shekaru 75 da suka gabata, manufofin kawar da sabani ta hanyar yin shawarwari, da daidaita rikici ta hanyar shiga tsakani, sun riga sun samu amincewa daga yawancin kasashen duniya.

Yayin taron, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da wani jawabi ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, nan gaba wato a cikin shekaru 75 masu zuwa, ya dace kasashen duniya su dauki mataki tare, domin tabbatar da manufar gudanar da harkokin kasashen duniya tsakanin bangarori daban daban, kuma ya gabatar da shawarwari guda biyar, wadanda ke hada martaba muhimmin matsayin MDD, da nacewa ka'idojin MDD, da nacewa manufar samun ci gaba cikin lumana, da nacewa manufar samun moriya ta hanyar gudanar da hadin gwiwa, da nacewa gina kyakkyawar makomar bil Adama.

Shugaban majalisar dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin kasashen Asiya na Bo'ao, kuma tsohon babban sakataren MDD Ban Ki-moon, shi ma ya yi jawabi yayin taron ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta sake yi wa bil Adam gargadi, cewa yanzu haka ya kamata kasashen duniya su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin dakile annobar tare. A cewarsa: "Gudanar da hadin gwiwa zai hada kan kasa da kasa, kuma ka'idojin MDD tushen ne na hadin gwiwar. A halin da ake ciki yanzu, hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa ya fi muhimmanci, duba da cewa wajibi ne kasashen duniyar su dauki mataki tare, wajen dakile cututtuka masu yaduwa, da sauyin yanayi, da sauran rikicin dake gaban bil Adam. Ina ganin cewa, muradun samun dauwamammen ci gaba na MDD, zai sa kasashen duniya su hada kai, yayin da suke fuskantar yanayi maras tabbas, da kalubalen yaduwar annobar COVID-19."

A nasa bangare, manzon musamman na firayin ministan jamhuriyar Malta, kuma zaunannenn wakilin kasar dake hukumar cinikayyar duniya wato WTO Alex Trigona, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, yanzu tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban ya gamu da kalubale, saboda kasar Amurka tana gujewa nauyin dake bisa wuyanta a cikin 'yan shekarun da suka gabata, inda matakan ficewa daga kungiyoyi da yarjejeniyoyin kasa da kasa da ta dauka suka lalata zaman karkon zamantakewar al'ummun kasashen duniya, yana mai cewa, "Ko shakka babu, tsarin gudanar da harkokin kasashen duniya tsakanin bangarori daban daban yana fuskantar kalubale, Amurka ta fice daga kungiyoyi da yarjejeniyoyin kasa da kasa da dama, lamarin da ya lalata tsari da zaman karko na kasa da kasa, har ya keta ka'idojin dokokin kasa da kasa, to ko wace kasa za ta samu moriya daga lamarin? Abun mai tabbas shi ne, yawancin kasashen duniya suna bukatar kwanciyar hankali, da dokokin kasa da kasa masu tabbaci, da tsarin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa mai inganci."

Bana ake cika shekaru 75 da kafa MDD, shekara mai zuwa kuwa za a cika shekaru 50 da maido da kujerar halal ta kasar Sin a MDD. Bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a dunya, kuma zaunanniyar mambar kwamitin din din din na kwamitin sulhun MDD, har kullum kasar Sin tana martaba muradun MDD, haka kuma tana sanya kokari matuka domin ciyar da bil Adam gaba cikin lumana.

Zaunanniyar mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed, ita ma ta godewa kasar Sin cikin sakonta ta kafar bidiyo, bisa goyon bayan da take nunawa MDD, tana mai cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana sauke nauyin kasa da kasa dake bisa wuyanta, tana mai cewa, "Shekara mai zuwa za a cika shekaru 50 da maido da kujerar halal ta kasar Sin a MDD. A cikin wadannan shekaru 50, har kullum kasar Sin tana taka babbar rawa a harkokin kasa da kasa. Misali akwai dakile matsalar sauyin yanayi, da gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma ingiza muradun samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 da sauransu."

Kungiyar MDD ta kasar Sin, da kungiyar diplomasiyya ta jama'ar kasar Sin ne suka shirya wannan taron kara wa juna sani cikin hadin gwiwa, wanda ya samu halartar masanan kasar Sin da na ketare sama da 100.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China