Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Birtaniya: Bikin cinikin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa zai jawo hankalin kasa da kasa
2020-09-01 13:36:22        cri


Za a gudanar da bikin cinikin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa na shekarar 2020 a farkon watan Satumba, a cibiyar taron kasar Sin dake birnin Beijing.

Masanin Birtaniya ta fuskar tattalin arziki, kana shugaban kungiyar 48 Group Club Stephen Perry, ya bayyana kwanan baya cewa, wannan aiki dake tafe, wani gaggarumin biki ne, a gabar da ake kokarin shawo kan cutar COVID-19, da samun wani ci gaba a duniya, kuma a karkashin halin da ake ciki na yadda Amurka ke kara sanyawa kasar Sin matsin lamba, wannan biki na da ma'ana matuka, wanda hakan ya sa shi jawo hankalin kasa da kasa sosai.

Shugaban kungiyar 48 Group Club, wanda ya taba karbar lambar yabo ta sada zumunta game da aikin kwaskwarima a kasar Sin Stephen Perry, ya shedawa manema labarai na CMG a kwanan baya cewa, bikin cinikin hada-hadar ba da hidima da za a yi a birnin Beijing, shi ne irinsa na farko a duniya a wannan bangare, wanda ya kasance wani muhimmin dandali na bude kofar kasar Sin ga duniya a fannin hada-hadar ba da hidima, kamar dai bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga ketare, da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na dandaloli mafiya girma na bude kofar kasar Sin ga ketare. Gudanar da wannan biki a karkashin halin rashin tabbas yanzu na da babbar ma'ana. Ya ce:

"A ganina, bikin a wannan karo zai samarwa kasar Sin damammaki masu kyau, da ma jawo hankalin kasa da kasa matuka. Musamman ma a halin da ake ciki na cutar COVID-19 da ta dabaibaye dukkanin fadin duniya, da yanayin fuskantar matsin lamba da kamfanin Huawei ke sha daga Amurka."

A ganinsa, kowa na iya ganin ci gaban da Sin take samun ta fuskar yakar cutar, Sin tana tsayin daka kan gudanar da wannan biki, duk da kangiya da ake fuskanta ta fuskar hada-hadar ba da hidima sakamakon bullowar cutar, matakin da ya bayyana matsayin da Sin take dauka na sauke nauyin dake wuyanta, game da farfado da tattalin arzikin duniya. Ya ce:

"Akwai wuya a gudanar da wannan biki a karkashin halin da muke ciki yauzu, Amma ina farin ciki sosai, da ganin yadda Sin ke iyakacin kokarin gudanar da shi, duk da halin tunkarar wasu matsaloli, matakin da zai taimawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya baki daya bayan barkewar cutar. Ina sa ran za a gudanar da wannan biki yadda ya kamata, ina imani da cewa, Birtaniya za ta shiga wannan aiki, za ta mara masa baya, saboda ya dace da muradun kasashen biyu."

Perry ya kara da cewa, Sin ta samu bunkasuwa ta a zo a gani, ta fuskar hada-hadar ba da hidima a shekarun baya-bayan nan, kana Birtaniya da kuma sauran kasashen yamma, na da fasaha da fifiko sosai a wannan fanni, don haka bangarorin biyu za su iya yin hadin kai, da kuma zurfafa mu'ammalarsu a wannan biki. Ya ce:

"Da farko dai, Sin za ta iya koyon sabon tunani a fannin nazari, da kuma ci gaba da kasashen yamma suke da shi a wannan fanni. Na biyu, bikin zai kasance wani dandalin fitar da kayayyaki, da hada-hadar hidimar kasashe zuwa ketare. Na uku kuma, dandalin zai samarwa kasar damammaki masu kyau, na shigo da wasu kayayyaki daga ketare. Saboda haka, a ganina, Sin za ta kara sanin ta game da kasuwar duniya ta wannan dandali, musamman ma kasuwannin kasashen yamma, don koyon darasi da fasahohi daga wajensu."

Yayin da ya tabo maganar bunkasuwar kasar Sin a shekarun dake tafe, Perry ya jadadda cewa, Sin da nahiyar Turai, sun samu ci gaba sosai wajen hadin kansu, bisa shawarar "ziri daya da hanya daya". Ya ce idan an yi hangen nesa, boyayyen karfi da Sin take da shi ta fuskar kirkire-kirkire, zai samu bunkasuwa nan gaba a duniya, saboda haka, kamata ya yi kasashen yamma su kara hadin kai da kasar Sin a wannan fanni.

Ya ce, a shekarun baya-bayan nan, Sin ta kauracewa yin ciniki da kuma zuba jari a kasashen yamma zuwa kasashe dake da alaka da shawarar "ziri daya da hanya daya", da ma kasashe masu tasowa, amma wannan bai nuna cewa, Sin ta dakatar da ciniki da kasashen yamma ba, Sin ta sauya manufar da take dauka a wannan fanni ne kawai. Kuma ta samu ci gaba mai kyau a fannin kasuwa tare da kasashe masu tasowa, kuma tana ci gaba da hadin kai da kasashen Turai.

Ya ce, "Amma, a ganina, ya kamata mu lura cewa, takunkumin da Amurka take sanyawa kamfanonin kasar Sin, musamman ma kamfanonin fasaha da kimiyar Intanet, zai kawo illa a cikin shekaru 3 ko 5 masu zuwa. Idan an yi hangen nesa, ba shakka Sin za ta samu ci gaba mai armashi ta fuskar kirkire-kirkire, kuma kamata ya yi kasashen yamma su kara hadin kansu da kasar Sin a wannan fanni." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China