Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zargin Da Aka Yi Wa Kasar Sin Dangane Da Batun Xinjiang Ba Shi Da Tushe
2020-08-30 00:07:32        cri

A wannan zamanin da muke ciki, Musulmai na kasashe daban daban suna shan wahala sosai, sakamakon yadda ake ta da yake-yake a wuraren da suke zama, da kuma jefa harkokin siyasan wuraren cikin yanayi na rudani. Lamarin da ya sa 'yan uwanmu Musulmai ke matukar shiga halin bakin ciki da samun bacin rai. A lokaci guda, ana jin labaran da wasu kafofin yada labaru suke watsawa cewa, gwamnatin kasar Sin tana mulkin danniya a jihar Xinjiang, inda take cin zarafin 'yan kabilar Uygur, wadanda yawancinsu Musulmai ne. Wannan magana ta sa Musulmai da dama suke nuna kin amincewa ga kasar Sin. Sai dai ba su yi tunani sosai ba, ko wannan zargin da aka yi wa gwamnatin kasar Sin gaskiya ne? Ko kuma akasin haka?

Yau bari mu duba zargin da aka yi wa kasar Sin, mu kuma yi bincike kan hakikanin yanayin da ake ciki, don neman sanin gaskiyar lamarin.

Da farko dai, wani zargin da ake yiwa gwamnatin kasar Sin shi ne, wai ta hana Musulmai 'yancin bin addininsu. Ko, wannan gaskiya ne? Hakika kundin tsarin mulkin kasar Sin ya kayyade cewa, dukkan 'yan kasar suna da cikakken 'yancin bin addini, wanda sauran kungiyoyi da mutane ba su da ikon hana shi. Maimakon danna Musulmai, hukumar jihar Xinjiang ta kasar Sin ta yi kokarin samar da hidimomi ga masu bin addinin Musulunci, inda ta kafa kwalejin nazarin Al'kurani, da sauran sassansa guda 8, da buga Al'kurani da wasu harsunan kabilu 4, da kokarin taimakawa Musulmai zuwa hajji a kasar Saudiya, ta hanyar shirya musu jirgin sama na musamman.

Na biyu, wasu sun ce wai gwamnatin kasar Sin tana rushe wasu masallatai don hana Musulmai taruwa da addu'a. Amma hakikanin abun da ya faru, shi ne ana kokarin gudanar da kwaskwarima kan wasu tsoffin masallatai, ko kuma idan ginin ya tsufa sosai, ba a iya gyarawa ba, to, sai a rushe shi, sa'an nan a gina wani sabon masallacin. Saboda haka, zargin da ake yi wai kasar Sin ta hana Musulmai damar yin amfani da masallaci ba shi da tushe ko kadan.

Wani zargi na daban da ake yi wa kasar Sin shi ne, cewa wai kasar ta kafa wasu sansanin gwale-gwale, inda aka kulle miliyoyin 'yan kabilar Uygur a ciki, tare da azabtar da su. To, zargin ya kan sanya mutane tunani cewa me ya sa hukumar kasar Sin ke kin jinin 'yan Uygur kamar haka? Amma hakikanin abun da ya faru shi ne, maimakon kafa "sansanin gwale-gwale", an kafa cibiyoyin koyar da ilimin sana'a a jihar Xinjiang. Makasudin wannan mataki shi ne, baiwa matasa na kabilu daban daban damar koyon fasahohin aiki, da al'adun kasar Sin, da nisanta su da tunani mai ban hadari na kaifin kishin Islama. Ta yadda za a samu damar kawar da ta'addanci daga tushe. Cibiyoyin da suka yi kama da wannan cibiyar kasar Sin, ana samunsu a kasashe daban daban, da suka hada da Birtaniya, da Amurka, da Faransa, da dai sauransu. Amma ba a taba zargin wadannan kasashe cewa sun kafa sansani don azabtar da mutane ba. Kun ga an nuna bambanci sosai game da wannan batu, tsakanin kasar Sin da kasashen yammacin duniya.

Wasu alkaluman da aka samu za su taimaka wajen ba mu wani tunani mai dacewa game da jihar Xinjiang. Daga shekarar 2010 zuwa ta 2018, adadin 'yan kabilar Uygur a yankin ya karu daga miliyan 10 da dubu 171 da dari biyar zuwa miliyan 12 da dubu 718 da dari hudu, inda ake samun karuwar da ta kai kaso 25.4 bisa dari. Wannan karuwar ta fi ta sauran kabilu daban daban na kasar Sin. To, tambayar ita ce, idan da gaske ne ana yi wa 'yan kabilar Uygur danniya a nan kasar Sin, to, shin ana iya samun karuwar al'ummar kabilar kamar haka? Wannan misali ya nuna mana cewa, ya kamata a dinga yin bincike don tabbatarwa yayin da muke sauraron wasu labaran da aka watsa, musamman na labaran da ake watsawa dangane da kasar Sin. Ta haka, za mu samu karin damammakin sanin ainihin abun da ya faru, maimakon baiwa wasu mutane damar yaudarar mu, da yin amfani da mu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China