Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabuwar manufa za ta tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin
2020-08-29 16:45:21        cri
A ranar 21 ga watan Yulin da ya gabata, a yayin wani taron karawa juna sani, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada wa masu tafiyar da masana'antu cewa, dole ne a kafa wani sabon salon bunkasa tattalin arzikin kasar, wato ya kamata a kara maida hankali kan bunkasa kasuwannin cikin gidan kasar, ta yadda za a iya bunkasa kasuwannin cikin gida da na waje tare. Sannan a ranar 24 ga watan Agusta, a yayin taron karawa juna sani, inda wasu nagartattun masana tattalin arziki da zaman al'umma na kasar Sin suka halarta, shugaba Xi Jinping ya sake jaddada wannan ra'ayin nasa. Har ma a yayin taron hukumar siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS da aka shirya a ranar 30 ga watan Yulin, an tsaida kudurin fitar da wannan sabuwar manufar tabbatar da bunkasa tattalin arzikin kasar Sin.

Kawo yanzu ana kokarin dakile cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya. Tattalin arzikin wasu kasashen duniya, ciki har da na kasashen Amurka da Japan ya ragu sosai. Tattalin arzikin kasar Sin ma ya ragu da kashi 1.6 cikin dari bisa na kwatankwacin lokacin bara. Ko menene dalilin da yasa kasar Sin ta sa niyyar sauya salonta na neman ci gaban tattalin arzikinta a halin yanzu? Na ga akwai wasu dalilan da suka sanya gwamnatin kasar Sin ta sa wannan niyya.

A baya, kasar Sin ta fi maida hankali kan kasuwannin ketare, a kowace shekara ta kan fitar da kayayyaki masu tarin yawa zuwa kasuwannin ketare, musamman a kasuwannin kasashen yammacin duniya. Amma bisa "Rahoto game da hasashen tattalin arzikin duniya" da asusun bada lamuni na kasa da kasa IMF ya fitar kwanan baya, an yi hasashen cewa, a shekarar 2020, tattalin arzikin kasashen duniya zai ragu da kashi 4.9 cikin dari, har ma tattalin arzikin kasashe masu arziki zai ragu da kashi 8 cikin dari sakamakon yaduwar annobar COVID-19. Sannan bisa alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar kwanan baya, an bayyana cewa, yawan darajar kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasuwannin kasa da kasa ya ragu da kashi 4.9 cikin dari a farkon rabin shekarar bana bisa kwatankwancin lokacin bara.

Wadannan alkalumai sun alamta cewa, bukatun da ake da su a kasuwannin kasa da kasa ya ragu. A waje daya kuma, kasar Sin ita kanta ta kasance kamar wata kasaitacciyar kasuwa. Mr. Yao Jingyuan, tsohon kakakin hukumar kididdigar kasar Sin ya yi bayanin cewa, yawan masu tafiyar da harkokin tattalin arziki a kasuwannin kasar Sin ya kai fiye da miliyan 100, sannan yawan kwararru da masana wadanda suka gama karatu daga jami'a ya kai fiye da miliyan 170, bugu da kari, mutanen da yawan kudin shiga da suka samu ya kai matsakaciyar wadata sun kai fiye da miliyan 400, daga karshe dai, a sanin kowa ne, yawan mutanen kasar Sin ya kai fiye da biliyan 1.4, dukkansu sun zama muhimmin karfin sayayya a kasuwar kasar Sin.

Mr. Yao Jingyuan ya kara da cewa, bayan da kasar Sin ta yi shekaru 40 tana yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare, ta zama kasa daya tilo a duk fadin duniya wadda take da dukkan nau'o'in masana'antu, wato ita kanta tana iya samar da dukkan kayayyakin da ake bukata a kasuwa.

A cikin shekaru 40 ko fiye da suka gabata, kasar Sin ta ci gajiyar manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare. Sakamakon haka, ko shakka babu, a lokacin da take kara maida hankali kan kasuwannin cikin gida, tabbas ne za ta kara maida hankali kan kasuwannin ketare, ta yadda za ta iya kara samun ci gaba bisa wadannan kasuwanni biyu. Muna da imanin cewa, bisa wannan sabuwar manufa, za a iya tabbatar da ganin tattalin arzikin kasar Sin ya kara samun ci gaba nan gaba. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China