Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar Pompeo a yankin Gabas ta Tsakiya ta nuna yunkurin siyasarsa
2020-08-28 20:50:08        cri

A jiya Alhamis ranar 27 ga wata, agogon wurin, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya kammala ziyararsa a kasashe hudu dake yankin Gabas ta Tsakiya. Yayin ziyarar ta sa, ba ma kawai ya yi kokarin yada manufar bangaranci ta Amurka ba, har ma ya shiga harkokin siyasa na cikin gidan Amurka, bisa matsayinsa na jami'in diplomasiyya, inda yunkurinsa shi ne shiga takarar shugaban kasa a nan gaba.

Kamar yadda aka lura, makasudin ziyararsa a yankin shi ne gurgunta matsayin kasar Iran. A ranar 14 ga watan Yulin shekarar 2015, kasashen Iran da Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Rasha, da Sin da Jamus, sun daddale wata yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran daga duk fannoni.

Bisa yarjejejniyar da suka daddale, Iran ta yi alkawari cewa, za ta kayyaden aikinta na sarrafa sinadarin nukiliya, domin neman amincewar kasa da kasa, su soke takunkumin da suka sanya mata. Daga baya kuma, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lambar 2231, inda aka tsai da cewa, wa'adin hana jigilar makamai da MDD ta sanyawa Iran zai kare a ranar 18 ga watan Oktoban shekarar nan ta 2020.

To sai dai kuma a yanzu, Amurka ta gabatar da daftarin shirin tsawaita wa'adin ga kwamitin sulhun MDD. Kuma abun takaici shi ne, kasa daya kacal ta jefa kuri'ar amincewa da shirin.

A sanadin haka, Pompeo yana ci gaba da kokari, inda har ya yi kira ga shugabannin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya cewa, ya dace su dakile mugun tasirin da Iran ke haifarwa tare. Kana ya wallafa wani rahoto a dandalin sada zumunta yana cewa, Amurka za ta maido da takunkumin da aka kakkabawa Iran tun daga ranar 20 ga watan Satumban dake tafe, lamarin da ya sabawa ra'ayin da mambobin kwamitin sulhun MDD suka cimma.

Abun da ya fi jawo hankalin jama'a shi ne, yayin ziyararsa a yankin Gabas ta Tsakiya, Pompeo ya halarci babban taron wakilan jam'iyyar Republican ta kafar bidiyo, kuma ya gabatar da wani jawabi, domin nuna goyon baya ga shugaban kasar mai ci yanzu.

Kan batun, jaridar "The Politico" ta Amurka ya gabatar da rahoto cewa, matakin da Pompeo ya dauka ya sabawa ka'idar kasar da aka kafa a cikin shekaru sama da goma. Wato bai kamata ba sakataren harkokin wajen kasar ya halarci taro na wata jam'iyya. A don haka, shugaban karamar tawagar da abin ya shafa ta majalisar wakilai ta Amurka ya sanar da cewa, za a gudanar da bincike kan lamarin, domin duba ko ya saba wa dokar kasar.

Hakika dai, ra'ayin kashin kai da Pompeo yake nunawa ya sa Amurkawan da yawansu ya kai sama da miliyan 300, suna damu matuka kan makomarsu. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China