Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu tabbas game da farfadowar tattalin arzikin kasar Afirka ta kudu
2020-08-28 14:08:04        cri

Kasar Afirka ta kudu kasa ce da annobar numfashi ta COVID-19 ta fi kamari a nahiyar Afirka. Kawo yanzu yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da annobar ya kai fiye da rabin wadanda suka kamu a dukkan kasashen Afirka. Sakamakon haka, tattalin arzikin kasar Afirka ta kudu wanda yake raguwa a kullum kafin bullar annobar, ya kara shiga mummunan hali, har ma ana hasashen cewa, ba shi da tabbas nan gaba kadan ba.

"Dokar hana sayarwa da shan barasa ta yi mini illa sosai, na rasa aikin yi sakamakon wannan doka. Ina cikin mawuyacin hali."

Lubabalo Mangcunyana, mai shekaru 27 da haihuwa, ya taba yin aiki a wata mashaya dake birnin Cape Town. A watan Maris na bana, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta fitar da wata doka, dake hana shan Barasa a duk fadin kasar domin rage yawan tashe-tashen hankula da masu shan Barasa suke tayarwa, ta yadda za a iya magance irin wadannan matsaloli wajen yin amfani da hidimomin likitanci da ake fatan za a yi amfani da su wajen ceton wadanda suka kamu da cutar COVID-19.

An rufe wuraren shan Barasa masu tarin yawa, sakamakon wannan doka, ya haifar da hasara sosai ga dukkan sana'o'in dake da alaka da Barasa a duk fadin kasar Afirka ta kudu. Alkaluma sun bayyana cewa, yawan mutanen da aikinsu yake da alaka da sana'ar sayar da Barasa, kuma suka rasa ayyukan yi ya kai dubu 120, sannan yawan kudin shiga da gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta yi hasara daga sana'o'in samar da kuma sayar da Barasa ya kai dalar Amurka miliyan 760. Alal misali, yawan hasarar da masana'antun dake samar da giyar Inabi, wato muhimmiyar sana'ar dake fitar da kayayyaki zuwa ketare, ta yi ya kai dalar Amurka miliyan 400, yayin da mutane dubu 20 suka rasa aikin yi.

Mr. Lucky Ntimane wanda ke kula da kungiyar masu sayar da Barasa ta Afirka ta kudu yana ganin cewa, mai yiyuwa ne hakikanin yawan mutanen da wannan doka ta shafa suna da yawa.

"Yawan mutanen da suke sana'o'in da suka shafi sayar da Barasa ya kai fiye da miliyan 1. Mutane da yawa daga cikinsu sun dogara kudin shigar da suke samu kan wannan sana'a, wannan ya alamta cewa, yawan mutanen da wannan doka ta hana shan Barasa ta yi musu tasiri ya kai wajen miliyan 5."

Halin da sana'ar sayar da Barasa a kasar Afirka ta kudu take ciki wani misali ne dake bayyana yadda tattalin arzikin kasar yake fuskantar kalubale. Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, tun bayan da aka fitar da dokar hana shan Barasa a karshen watan Maris zuwa yanzu, yawan mutanen da suka rasa aikin yi ya kai kimanin miliyan 1 da dubu 500, adadin ya alamta cewa, yawan marasa aikin yi a kasar, ya kai kashi 30 cikin dari na jimillar mutanen kasar.

Tito Mboweni, ministan kudin kasar Afirka ta kudu ya yi hasashen cewa, "A bana, saurin raguwar tattalin arzikin kasar Afirka ta kudu zai kai kashi 7.2 cikin dari. Ba a taba ganin irin wannan raguwar tattalin arzikin kasar Afirka ta kudu ba kusan shekaru 90 da suka gabata."

A farkon kaddamar da wannan doka, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta fitar da wasu matakan tabbatar da kiyaye bunkasar tattalin arziki. Alal misali, a watan Afrilu, shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ya sanar da wani shirin ware kudin kasar Rand biliyan 500, kwatankwacin dolar Amurka biliyan 30 domin bunkasa tattalin arziki. Amma wasu masana tattalin arzikin kasar sun yi zargi cewa, gwamnatin ba ta cika alkawarinta yadda ya kamata ba, har yanzu, Rand biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 60 kawai ta ware ga wasu masana'antun da suke bukatar tallafi. Mr. Duma Gqubule, wani kwararre kan ilmin tattalin arziki yana ganin cewa, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ba ta dauki matakai masu dacewa ba wajen dakile wannan rikicin tattalin arziki. Mr. Duma ya nuna cewa, shugaban kasar ya sanar da matakan bunkasa tattalin arziki a kan lokaci, amma a lokacin da ma'aikatar kudi take sanar da kasafin kudin da za a kebe, ta soke matakai da yawa. Ma iya cewa, a yayin da kasar ta tsunduna cikin rikicin tattalin arziki mafi kamari da ba ta taba gani cikin shekaru 100 da suka gabata ba, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ba ta dauki matakai masu dacewa ba.

Yanzu, yawan sabbin mutanen da suka harbu da cutar ya fara raguwa, kana gwamnatin kasar tana kokarin soke dokar hana shan Barasa da ta sanya sannu a hankali. Ana fatan tattalin arzikin kasar zai farfado har ma ya bunkasa kamar yadda ya kamata, sakamakon haka, mutane da yawa za su iya samun damammakin komawa bakin ayyukansu. Amma wasu masana tattalin arziki suna ganin cewa, bakin alkalami ya riga ya bushe, domin an riga an yiwa tattalin arzikin kasar Afirka ta kudu illa, a don haka, za a dauki dogon lokaci kafin tattalin arzikin kasar ya dawo halin da yake ciki a baya. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China