Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasar Amurka dake tayar da tarzoma a tekun kudancin Sin ba za su cimma buri ba
2020-08-27 20:55:23        cri

A jiya Laraba ne ma'aikatar kasuwancin Amurka, ta sake bayyana cewa, za ta dauki mataki kan kamfanonin kasar Sin da yawansu ya kai 24, bisa fakewa da batun gina tsibiri a tekun kudancin kasar Sin. A kuma wannan rana, ma'aikatar harkokin wajen kasar, ita ma ta tsai da kuduri cewa, ba za ta amince da samar da visa ga 'yan asalin kasar Sin, wadanda ke da hannu a cikin aikin gina tsibiri a yankin ba.

Duk wadannan sun nuna cewa, Amurka tana daukar sabbin matakan na tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin, lamarin da ya sabawa dokokin kasa da kasa, da ka'idar huldar kasa da kasa, kuma tabbas kasar Sin za ta mayar da martani domin kare 'yancin kanta, da tsaronta, da kuma moriyar ci gabanta.

Kowa ya san cewa, yankin tekun kudancin kasar Sin yana karkashin mallakar kasar Sin ne, a don haka, gina tsibiri a cikin yankin, hakkin kasar Sin ne, wanda bai dace Amurka ta nuna wani ra'ayi na ta kan hakan ba.

An lura cewa, a cikin 'yan kwanakin baya bayan nan, rikicin dake cikin kasar Amurka yana tsananta, kana takarar babban zabe a kasar ita ma tana kara tsanani. A lokaci guda kuma, 'yan siyasar kasar na mai da hankali kan batun tekun kudancin kasar Sin. Alal misali, Amurka ta aika manyan jiragen ruwa masu saukar jiragen sama guda biyu, domin su yi atisayen aikin soja a tekun kudancin kasar Sin, kana ta tura jiragen sama zuwa yankin dake kusa da tekun kudancin kasar Sin domin yin leken asiri, duk wadannan sun nuna cewa, Amurka tana son tayar da tarzoma a yankin, tare kuma da lalata huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashe makwabtan ta.

Amma ko shakka babu, Amurka ba za ta cimma burin ta ba. A hannu guda kuma ana sa ran cewa, Amurkar za ta daina tayar da tarzoma a yankin tekun kudancin kasar Sin, saboda ko kadan, kasar ta Sin ba ta jin tsoron dukkanin wani takunkumi da Amurka ke sanya mata. Kuma duk da cewa kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufar samun ci gaba cikin lumana, a daya bangaren ba zai yiwu ta amince da ketar da ake neman yi mata ba, kuma idan har 'yan siyasar Amurka suka ci gaba da daukar matakai kan ta, to kuwa tabbas za ta mayar da martani. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China