Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda aka cimma al'ajabi a Shenzhen
2020-08-26 20:01:17        cri

Ranar 26 ga watan Agustan bana, ake cika shekaru 40 da kafa yankin musamman na tattalin arziki na Shenzhen na kasar Sin. A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, Shenzhen ya samu babban ci gaba, har adadin GDPn birnin ya karu daga kudin Sin yuan miliyan 200 zuwa yuan triliyan 2.7 a yanzu.

Mujallar "The Economist" ta Birtaniya ta bayyana cewa, akwai yankunan musamman na tattalin arziki sama da 4000 a fadin duniya, amma al'ajabin Shenzhen ya kai sahun gaba.

To ko mene ne dalilin da ya sa birnin Shenzhen ya samu irin wannan ci gaba cikin saurin haka?

An taba bayyana saurin aikin birnin kamar haka: an kammala gina hawa guda na babban gini cikin kwanaki uku kacal, mutanen dake aiki a birnin suna ganin cewa, lokaci kudi ne, saurin aiki rayuka ne, a sanadin haka, mazauna birnin suna cike da kuzari yayin aiki karkashin manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare a kasar ta Sin.

Hakika har kullum kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, suna taka babbar rawa wajen ci gaban birnin, wato tun daga shekarar 2000, birnin ya kara mai da hankali kan fasahohin zamani, amma kafin wannan, an fi mai da hankali kan aikin samar da kayayyaki da cinikayya. Kawo yanzu an riga an kafa tashoshin fasahar 5G sama da dubu 46 a birnin, inda har birnin ya kasance na farko a fadin duniya a fannin yin amfani da fasahar 5G daga duk fannoni.

A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, ba ma kawai Shenzhen ya yi kokarin raya kansa ba ne, har ma ya samar da damammaki ga sauran kasashen duniya. Wato dai tun daga shekarar 1993, adadin shige da fice na birnin ya kai sahun gaba a fadin kasar Sin.

A bayyane take cewa, idan a lura ci gaban birnin Shenzhen alama ce ta ci gaban kasar Sin, tun bayan da ta fara aiwatar manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare, haka kuma alama ce ta ci gaban da al'ummun Sinawa suka samu, kan hanyar tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin karkashin jagorancin JKS.

Ana iya cewa, Shenzhen ya nuna wa daukacin kasashen duniya kuzarin kasar Sin, wajen raya tsarin gurguzu mai halayyar musamman. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China