Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Trump za ta dandana kuda kan matakan da ta dauka
2020-08-24 16:31:44        cri

A yau ne, kamfanin ByteDance na kasar Sin, wato kamfanin dake mallakar Tik Tok ya sanar da cewa, zai gurfanar da gwamnatin Trump a gaban kotu a hukumance a ran 24 ga watan. Kamfanin ByteDance ya gabatar da sanarwa a yau da safe da karfe 10 da minti 55 a kan shafin Weibo nasa, inda ya bayyana cewa, a cikin shekara kimanin daya da ta gabata, ya nuna sahihanci don neman yin mu'amala da gwamnatin kasar Amurka, da gabatar da shirin daidaita matsalar dake kasancewa a tsakaninsu. Amma gwamnatin kasar Amurka ta yi watsi da hakikanin batun, kuma ta yi yunkurin shiga tattaunawar dake tsakanin kamfanonin ciniki kai tsaye ba tare da la'akari da dokoki ba. Don tabbatar da hakkin kamfanin da na masu amfani da hidimar kamfanin, ByteDance ya sanar da gurfanar da gwamnatin Trump a gaban kotu a hukunce.

A sakamakon takaddamar ciniki dake tsakanin Sin da Amurka, an kawo illa ga sha'anin kimiyya da fasaha, kuma kamfanin ByteDance na kasar Sin ya tinkari matsaloli da dama. A ranar 7 ga wannan wata, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan umurnin shugaba, inda ya ce, bayan kwanaki 45, za a sa ido ga duk kamfani ko mutanen da suke yin ciniki tare da kamfanin ByteDance na kasar Sin dake mallakar Tik Tok da kuma kamfanin Tencent dake mallakar Wechat, ministan ciniki na kasar Amurka zai dauki alhakin tsara ka'idojin gudanar da aikin. Shugaba Trump ya bayyana wai cewa, kamfanin Tik Tok ya tattara bayanai daga mutanen Amurka da suka yi amfani da manhajar, za a samar da sauki ga gwamnatin kasar Sin wajen yin leken asiri a fannin ciniki. A wannan rana da dare, kamfanin ByteDance ya sanar wa kasar Amurka cewa, idan gwamnatin kasar Amurka ba ta nuna adalci gare shi ba, zai gurfanar da gwamnatin a gaban kotun Amurka.

Amma gwamnatin kasar Amurka ta ci gaba da hana ayyukan Tik Tok. A ranar 14 ga wannan wata, Trump ya sa hannu kan dokar ofishin shugaban kasa wato ya sa kamfanin ByteDance ya sayar da manhajar Tik Tok ga kasar Amurka a cikin kwanaki 90. Bisa binciken da aka yi, darajar harkokin Tik Tok a kasar Amurka ta kai dala biliyan 20 zuwa 50, kuma ya zuwa yanzu yawan mutanen da suke amfani da mahajar Tik Tok a kasar Amurka ya zarce miliyan 100. Ya zuwa yanzu, kamfanin Microsoft na kasar Amurka ya tabbatar da yin shawarwari kan sayen harkokin Tik Tok, kamfanonin Alphabet, da Oracle da Twitter sun yi bincike da la'akari da saye ko rashin sayen. A jiya wasu kamfanonin Amurka sun yi tattaunawa kan hada kai da kafa wata kungiya don zuba jari ga harkokin Tik Tok.

Kamfanin Tik Tok ya shirya mayar da martani ga umurnin da shugaba Trump ya bada, a ganinsa matakan da aka dauka na hana shi yin ciniki tare da kamfanonin Amurka ba su dace da doka ba. Ya zuwa yanzu, kamfanin Tik Tok dake kasar Amurka ya ce babu ma'aikatan kamfanin da za su sanar da janyewa daga aikinsu a kamfanin.

A yau ne, kamfanin Byte Dance dake mallakar TikTok ya shirya sosai, da bayar da sanarwar gurfanar da gwamnatin Trump a gaban kotu. Babu shakka, gwamnatin kasar Amurka ta tilasta yin ciniki ba tare da adalci ba, za ta dandana kudarta kan matakan da ta dauka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China