Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Tibet ya taimakawa manoma da makiyaya 543,000 samun ayyukan dogaro da kai
2020-08-24 10:48:48        cri

Yankin Tibet mai cin gashin kai dake shiyyar kudu maso yammacin kasar Sin ya tallafawa manoma da makiyaya kimanin 543,000 wajen samar musu ayyukan dogaro da kai a watanni bakwai na farkon wannan shekarar, hukumomin yankin sun tabbatar da hakan.

A cewar sashen kula da ma'aikata da kyautata rayuwar al'umma na yankin, ayyukan suna iya samar da kudaden shiga da ya zarce Yuan biliyan 3.9, kwatankwacin dala miliyan 564.

Tibet ya bullo da shirye-shirye masu yawa a wannan shekara domin taimakawa manoma da makiyaya, sun kasance muhimmin bangaren dake samar da ayyukan kwadago ga shiyyar, an samar da guraben ayyukan yi da karin kudaden shiga, wanda ya hada da samar da tallafi ga daidaikun mutane da masu kafa sana'o'i. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China