Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa Na Kara Jin Dadi Sakamakon Ingancin Ruwan Sha
2020-08-22 20:45:40        cri

Ya zuwa karshen watan Yunin bana, an kammala ayyukan samar da ruwan sha mai inganci a gundumomi bakwai da suka fi fama da kangin talauci a nan kasar Sin, kuma gaba daya, kasar ta zuba jari na Yuan biliyan 198.4 wajen gina ababen more rayuwa a fannin samar da ruwan sha a yankunan karkarar kasar, mutanen kauyuka sama da 80% suna amfani da ruwan famfo a halin yanzu, kuma, ingancin ruwan ya kyautata sosai, wannan ya nuna cewa, kasar Sin ta cimma nasara ta karshe wajen samar da tsabtaccen ruwan sha ga mutane masu fama da talauci.

 

 

Ruwa, asali ne na rayuwa, shi ne kuma tushe na fitar da kayayyaki, zaman rayuwa da kuma muhallin halittu. A nan kasar Sin, yawancin wurare masu fama da talauci suna yankin dutse, kuma ba ma iya samun isasshen ruwa, sannan manyan na'urorin samar da ruwa ba su da kyau, hakan ya sa rashin isasshen ruwa da rashin ingancin ruwan sha sun taba kasancewar babbar wahalar da mazauna wurin suka fi fuskanci, da babbar matsala da yankunan suke fuskanta wajen samun ci gaba. Saboda haka, warware matsalar rashin ingancin ruwan sha da mutane masu fama da talauci a kauyuka suke fuskanta, ya zama wani muhimmin sashe ne na ayyukan kawar da talauci na duk fadin kasar, wanda aka mayar da shi a matsayin wani muhimmin aiki mai ma'ana kwarai.

Ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin tana mayar da hankali kan warware matsalar. Musamman ma tun bayan shekarar 2016, bayan an dauki jerin matakai masu dacewa, an kara matsayin aikin samar da isassun ruwa ga mutanen dake zama a kauyuka kimanin miliyan 256, inda ta warware matsalar karancin ruwan sha ga mutane masu fama da talauci kimanin miliyan 17.1. lamarin da ya sa, aka warware matsalar karancin ruwa baki daya. Daga halin babu ruwan sha zuwa na samun isasshen ruwan sha, har ma zuwa na samun ingancin ruwan sha, irin ci gaban da kasar Sin ta samu, ya bayyana ra'ayin gwamnatin kasar na dora muhimmanci kan zaman rayuwar jama'arta.

 

 

Bisa kokarin da ake yi na warware matsalar rashin isasshen ruwan sha da matalauta ke fuskanta, jama'ar dake yankuna masu fama da talauci suna kara jin dadin zaman rayuwarsu, kuma ana karfafa harsashi na neman ci gaban sana'o'i daban daban, ta yadda mazauna yankunan suka kara imaninsu kan kawar da talauci da nema wadata, don ciyar da zaman rayuwarsu gaba.

Amma, warware matsalar ba shi ne buri na karshe na kasar Sin ba. A ganin gwamnatin kasar, ya kamata a kara sa ido kan ayyukan samar da ruwan sha na wadannan yankuna, da kara inganta nasarorin da aka cimma wajen kawar da talauci, kana da hana sake bullar matsalar rashin isasshen ruwa, da ci gaba da tsara wani shirin kulawa da gudanarwa na ayyukan samar da ingancin ruwan sha a kauyuka. Dole ne a tabbatar da samar da ruwan sha mai tsabta ga mazauna kauyuka a kullum. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China