Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin bangarori uku ya fara taro game da samar da daftarin yarjejeniya kan batun madatsar ruwan Habasha na tekun Nile
2020-08-22 16:34:19        cri
Ma'aikatar noman rani da albarkatun ruwa ta kasar Masar tace, kwamitin kwararru da masana shara'a na bangarorin kasashe uku sun fara taro a ranar Juma'a don samar da daftarin yarjejeniya kan batun gina madatsar ruwa ta kasar Habasha wato GERD a takaice.

A cewar ma'aikatar, kawo yanzu an tsara kwarya-kwaryar daftarin, ta kara da cewa, daftarin ya kunshi bukatun kowace kasa daga cikin kasashen uku wanda ya shafi muhimman batutuwan da suka amince da su da kuma wadanda basu amince dasu ba.

Ministocin kula da noman rani da albarkatun ruwa na kasashen Masar, Sudan da Habasha, su kuma halarci wani taron ta kafar bidiyo wanda kungiyar tarayyar Afrika AU ta shirya domin dawowa teburin sulhu da nufin cimma yarjejeniya game da batun gina madatsar ruwan ta GERD.

Aikin madatsar ruwan na GERD wanda zai lashe kudi dala biliyan 4, ya zamanto wani tushen rikici kan batun tekun Nile, tun bayan da kasar Habasha ta fara aikin gina shi a shekarar 2011.

Habasha tana sa ran madatsar ruwan zata samar da hasken lantarki sama da mega watt 6,000, kuma idan aikin ya kammala zai kasance tashar samar da lantarki ta ruwa mafi girma a Afrika.

Sai dai kuma, Masar, wacce ke bangaren karshen kogin na Nile ta dogara ne kan kogin wajen samun ruwan da take amfani dashi, ta nuna damuwa matuka bisa abinda ta kira cewa, aikin zai iya shafar albarkatun ruwan da take amfani dashi da yawansa ya kai kubik mita biliyan 55.5 a duk shekara.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China