Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi yana dora muhimmanci kan kiyaye muhallin halittu yayin da kasarsa ke samun habakar tattalin arziki
2020-08-21 16:06:33        cri

A kwanan nan, babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping, ya ziyarci birnin Hefei, fadar mulkin lardin Anhui dake gabashin kasar.

Yayin wannan ziyara, shugaba Xi ya duba wani sashe na madatsar ruwa dake gundumar Feidong, inda ya ganewa idanunsa yanayin gudanar tafkin Chaohu, ya kuma jinjinawa masu aikin yaki da ambaliyar ruwa a yankin, wadanda suka kunshi dakarun sojin kasar Sin na PLA, da kuma rukunin 'yan sanda masu dauke da makamai.

Shugaban na Sin ya kuma jaddada cewa, bayan aukuwar ambaliyar ruwa, bai kamata mutane su shiga wuraren da aka kebe musamman domin tattara ruwa ba. Saboda idan ana son samun zaman jituwa tsakanin dan Adam da muhalli, ya zama tilas a kiyaye muhallin halittu, gami da dimbin albarkatun da Allah ya hore mana.

Shugaba Xi yana maida hankali sosai wajen kiyaye muhallin halittu, sa'ilin da kasarsa ke samun ci gaba cikin sauri a wadannan shekaru. Alal misali, Xi ya bayyana cewa, "ni'imtattun wurare masu kyan muhalli su ne ke kawo alfanu ga bunkasar tattalin arziki". Wato babu sabani tsakanin kiyaye muhalli da bunkasa tattalin arziki, ke nan idan muhallin halittu ya lalace, tattalin arziki da zamantakewar al'umma ma za su samu koma-baya.

Har wa yau, shugaba Xi Jinping ya taba nuna cewa, kyan muhallin halittu zai samar da zaman jin dadi ga al'umma. Daidaita matsalolin da suka shafi gurbata muhallin halittu, zai taimaka sosai ga kyautata zaman rayuwar al'umma da kara biyan bukatunsu na yau da kullum.

Shugaba Xi ya kuma ce, idan muhallin halittu ya kyautata, al'adu za su bunkasa, in aka samu akasin haka, al'adu za su tabarbare. Wato a cewarsa, raya kyakkyawan muhallin halittu na da alaka ta kut da kut da dauwamammen ci gaban kasar Sin da ma daukacin al'ummarta baki daya. Xi ya kuma jaddada cewa, ya kamata a kara fadakar da al'umma kan muhimmancin kiyaye muhallin halittu, saboda abu ne da ya shafi zuriyoyin dake tafe.

Bayan haka kuma, shugaba Xi ya taba bayyana cewa, batun kiyaye muhallin halittu, muhimmin batun siyasa ne wanda ya shafi babban nauyin dake wuyan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana muhimmin batu ne wanda ya shafi zamantakewar al'umma baki daya. Xi Jinping da sauran wasu manyan shugabannin kasar Sin da na jam'iyyar kwaminis suna bakin kokarinsu domin daukar matakan samar da wani kyakkyawan muhallin halittu ga jama'ar kasar, musamman a daidai lokacin da ake gina zaman al'umma mai matsakaiciyar wadata a kasar ta Sin.

Bugu da kari, a karkashin shugabancin Xi Jinping, kasar Sin tana kokarin yayatawa duk duniya dabarunta na tinkarar matsalar lalacewar muhallin halittu, ciki har da fadada hadin-gwiwa da kasashe daban-daban, musamman kasashen dake tasowa a fannin magance matsalar sauyin yanayi gami da kwararar hamada. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China