Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka za su tattauna ta wayar tarho cikin kwanaki masu zuwa
2020-08-20 21:05:01        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng, ya bayyana Alhamis din cewa, cikin 'yan kwanaki masu zuwa, kasashen Sin da Amurka sun amince za su tattauna ta wayar tarho.

Gao ya bayyana haka ne, lokacin da aka nemi ya yi Karin haske game da rahotannin dake cewa, nan ba da dadewa ba, kasashen biyu za su gudanar da tattaunawa, don tantance irin ci gaban da aka samu bayan da suka daddale yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya a mataki na farko a tsakaninsu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China