Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar shugaba Xi a Anhui na kara haska burin kasar Sin na gina al'umma mai matsakaiciyar wadata
2020-08-20 17:27:30        cri

Kasancewar a bana kasar Sin ke kammala wa'adin da ta tsara, na gina al'umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkanin fannoni, da kuma shirinta na yaki da talauci, shugabanninta a matakai daban daban, na kara azama wajen sanya ido, da tabbatar da kammala wannan manufa cikin nasara.

Karkashin wannan manufa ne kuma, shugaban kasar Xi Jinping ke ziyartar yankunan kasar daban daban, ciki hadda wurare da ake yaki da ambaliyar ruwa, wadda a yanzu haka ke addabar wasu sassan kasar, tare da jaddada kudurin gwamnatinsa, na tsame daukacin al'ummun kasar daga kangin talauci, duk da kalubalen cutar COVID-19 da kasar ta fuskanta a baya bayan nan.

Ko da a ranar Talata 18 ga watan nan na Agusta ma, sai da shugaban kasar ya gudanar da muhimmiyar ziyara a lardin Anhui dake gabashin kasar. Ziyarar da ta kunshi ganewa idanun sa yanayin da kogin Huaihe ke ciki, kogin da bisa taswirar kasar ya raba arewaci da kudancin Sin. Ya kuma ziyarci ganuwar ruwa ta Wangjiaba, domin nazarin tasirin ta ga kogin na Huaihe, da kuma matakan kandagarkin ambaliyar ruwa, da ayyukan jin kai da ake aiwatarwa a mazaunan al'ummar dake makwaftaka da wannan kogi, tun bayan fara fuskantar bala'in ambaliyar a farkon shekarar nan ta bana.

Baya ga wannan, shugaba Xi ya ziyarci kamfanin hada jakukkuna na Hongliang dake garin Wangjiaba, don ganin yanayin farfadowar ayyuka bayan shan fama da cutar numfashi ta COVID-19.

A zangon karshe na wannan ziyara, shugaba Xi Jinping ya isa Xitianpo Zhuang Tai na kauyen Limin dake garin Cao Ji. Ya kuma ziyarci filayen noma, domin kara fahimtar halin da gonaki ke ciki. A kauyen Xidanpo na gundumar Funan, dake birnin Fuyang, shugaban ya gana da al'ummun da ke zaune daura da filayen noma. Tsaye cikin garjin rana, shugana Xi ya bayyana cewa, "Ina matukar damuwa game da halin da al'ummar mu ke ciki a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, amma a duk lokacin da na ga wadannan mazauna yankunan karkara na samu madogara, da karfin gwiwar ci gaba da ayyuka da rayuwa, na kan ji sauki a rai na."

Muhimman abubuwa da za mu iya lura da su game da wannan ziyara da shugaban na Sin ya kai wannan lardi, sun hada da yadda har kullum mahukuntan kasar ke kokarin sauke dauyin dake wuyan su, na lura da cimma nasarar dukkanin wasu manufofi da aka tsara aiwatarwa domin ci gaban al'umma. Kaza lika muna iya lura da himma da kwazon da Sinawa ke dorawa ga ayyukan yaki da bala'u daga indallahi, da ma wadanda ayyukan bil Adama ka iya haifarwa. Bugu da kari, har kullum kasar Sin na dagewa wajen kare muhalli, da tabbatar da samar da muhalli mai nagarta ga al'umma, musamman talakawa dake huskantar nau'oi mabanbanta na kalubalen rayuwa.

Alal hakika, abun ban sha'awa ne ganin yadda shugabanni irin na babbar kasa kamar Sin, ke iya ware lokacin cikin tarin hidimomin dake gaban su, domin cudanya da al'ummun dake rayuwa a matakin farko wato na kauyuka, da yankuna mafiya fama da talauci.

A daya bangaren kuma, sanin kowa ne cewa cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar da babban kalubale ga fannonin tattalin arziki a dukkanin sassan rayuwar bil Adama, amma duk da haka, mahukunta a kasar Sin ba su yi kasa a gwiwa ba, wajen jagorantar aiwatar da matakai na farfadowa da harkokin sarrafa hajoji a masana'antu, aikin da ke tafiya kafada da kafada da matakan kandagarki da dakile sake bullar wannan cuta tsakankanin al'ummar kasar.

Ko shakka babu, ziyarar da shugaba Xi Jinping ya gudanar a lardin Anhui, ta kara haskakawa duniya kwazon kasar Sin, game da burinta na gina al'umma mai matsakaiciyar wadata, da himmar fitar da daukacin Sinawa daga matsanancin yanayi na fatara. Baya ga fatan ci gaba da fadada hada hadar sarrafa kayayyakin masana'antu, da kula da muhallin halittu yadda ya kamata. Kari kan hakan, Sin ta amince ta fuskanci duk wani kalubale da ka iya bijirowa, a wannan hanya ta wanzar da ci gaba mai dorewa da take fatan cimmawa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China