Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen yamma na kara jin kunya game da karyar da suke yi a kan yankin Xinjiang
2020-08-19 17:42:17        cri

A baya, saboda wata manufa ta neman biyan bukata, wasu kasashen yamma, musamman Amurka ke ta neman shafawa kasar Sin kashin kaji kan yanayin kare hakkin dan-Adam, da ma shiga harkokinta na cikin gida ta fannoni daban-daban, da manufofinta na tafiyar da harkokin jihar Xinjiang, lamarin da ya sanya al'ummar Sinawa da ma al'ummar kabilu daban daban na jihar kimanin miliyan 25 yin Allah wadai da nuna adawa da wannan mataki, haka ma al'ummar kasashen duniya masu nuna gaskiya da adalci sun soki matakin na Amurka.

Duk mai bibiyar abubuwan dake faruwa a jihar, ya san cewa, bisa managartan matakan da aka dade ana dauka a jihar Xinjiang, kan yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a 'yan shekarun da suka gabata, ya sanya jihar shiga cikin sabon zamani na samun wadata da ci gaba.

Alkaluman da hukumar kwastam mai kula da tashar layin dogo ta Alataw Pass, dake jihar Xinjiang a arewa maso yammacin kasar Sin ta fitar, sun nuna cewa, adadin hajojin da aka yi sufurinsu ta layin dogon yankin ya kai sama da miliyan 25, wadanda kuma darajarsu ta haura dala miliyan 80, tun bayan bude hada-hadar cinikayya ta yanar gizo, da safarar kayayyaki zuwa kasashen ketare ta tashar a watan Janairun bana.

Wannan ya sake karyata ikirarin da kasashen yamma ke yi game da rashin kwanciyar hankali a yankin. Abin tambaya a nan shi ne, idan har babu zaman lafiya kamar yadda kasashen yamma ke yada jita-jita, ta yaya za a a samu wannan ci gaba? Ai dama gaskiya ba ta buya.

Hada-hadar sufurin hajoji tsakanin Sin da Turai ta jiragen kasa ta tashar Alataw Pass ta samu bunkasa a bana, inda a yanzu haka jiragen kasan dakon hajoji dake bin hanyoyi 15 ke bin wannan tasha.

Rahotanni sun nuna cewa, an yi jigilar kayayyakin wasan yara, da gadaje da kujeru na katako, da tufafi, da sauran kayayyakin bukatu na yau da kullum, ta hanyar cinikayya ta yanar gizo zuwa kasashen Belgium, da Netherlands, da Jamus da sauran kasashen tarayyar Turai ta wannan tasha.

Wannan na nuna cewa, cinikayyar yanar gizo tsakanin kasashen ketare, wani sabon salo ne na cinikayyar waje, wanda ya samar da tallafi wajen habaka tattalin arzikin cikin gidan kasashe, tare da inganta cudanyar tattalin arziki.

A don haka, yanzu haka jihar Xinjiang na cikin wani lokaci mafi kyau na samun wadata da bunkasuwa a tarihi, da tabbatar da 'yancin jama'ar kabilu daban daban dake jihar a fannoni daban daban, ciki har da ikon rayuwa da na samun ci gaba, sabanin karya da jita-jita marasa tushe da ake watsa kan yankin na Xinjiang. Wadannan nasarori da jihar ta samu, ya kara nunawa duniya cewa, duk maganganun da kasashen yamma ke yi a kan yankin, makirci ne da manufurci irin nasu kawai. Hausawa na cewa, manufurcin Dodo, ya kan ci mai shi.(Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China