Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manoman kasar Sin suna amfani da fasahar zamani don kyautata zaman rayuwarsu
2020-08-17 14:01:25        cri

A shekarun baya, manoman dake lardin Fujian na kasar Sin sun yi amfani da fasahohin zamani masu alaka da yanar gizo ta Internet wajen sayar da 'ya'yan itatuwa da ganyen shayi na Ti, lamarin da ya sa su samun karin kudin shiga, da damammakin kyautata zaman ryauwarsu.


Yanzu haka wani lokaci ne da ake samun dimbin inabi a garin Saiqi na birnin Ningde dake lardin Fujian. Da safiyar ko wace rana, Madam Chen Guilian da iyalinta su kan tafi gandunsu na inabi don tsinkar inabi. Sa'an nan, a duk lokacin da ta shiga gandun, Madam Chen ta kan fara watsa bidiyon dake nuna yadda take aiki kai tsaye a kan shafin Internet, ta hanyar amfani da wayar salularta.

A cewar Madam Chen, lokacin da ta fara sayar da inabi, ta taba yin wannan aiki a cikin wani shago, da kuma yin ciniki na sari. Inda ta ce ayyuka ne masu wahala, sa'an nan kudin shigar da ta samu ba yawa. Daga bisani, ta ga akwai damar sayar da kaya ta yanar gizo ta Internet, don haka ta fara bude wani kanti kan shafin Internet, don sayar da inabi. Har ma ta fara watsa hotunan bidiyo don tallar inabinta. Lamarin da ya taimaka mata sayar da inabi sosai.

"Yanzu yawan inabin da nake sayarwa a rana guda, ya fi wanda na sayar cikin wata daya a baya. Yadda fasahar sayar da kaya ta hanyar watsa bidyon kayan kai tsaye a shafin Internet ke samun ci gaba a nan kasar Sin, ya sa na ga akwai damar yin amfani da wannan fasaha, don nuna wa jama'a inabinmu, da muhallinmu, da fasahohin da muke amfani da su wajen shuka inabi da tsinkar su."

Yadda Madam Chen ke samun ci gaba a harkar sayar da inabi, ya nuna cewa manufar raya aikin sayar da kaya a shafin Internet tana taimakawa manoma samun karin kudin shiga. Cai Longyu, wani jami'i ne na garin Saiqi, wato garin Madam Chen, wanda ya ce zuwa yanzu mutanen garinsu fiye da 1000 suna sayar da kaya a shafin Internet.

"Wannan aiki na sayar da kaya ta shafin Internet ya ba mu damar samar da karin guraben aikin yi, da taimaka mana raya sana'ar shuka inabi, da samar da karin kudin shiga ga manoma. Bisa wannan mataki, za mu samu cimma burin raya tattalin arzikin kauyuka, da samun zaman rayuwa mai inganci."

Lardin Fujian yana cikin wasu wuraren kasar Sin da ake samun ganyen shayi na Ti mai kyau, sai dai a wannan wuri, an fi samun daidaikun manoman da suke shuka ganyen shayi da sayar da su da kansu, maimakon samun wasu kamfanoni da za su kula da aikin sayarwa. Lamarin da ya sanya manoman kasa sayar da kayansu kan wani farashi mai kyau. Daga bisani, wani mutum mai suna Wang Mingxiu ya zo wurin, tare da shirin daidaita wannan yanayin da ake ciki.

"Na zo wannan kauye ne shekaru 6 da suka wuce, sa'an nan na kafa wannan kamfani don taimakawa aikin samar da ganyen shayi da sayar da su, tare da wani buri na rage talauci."

Wani tsarin da mista Wang ya kirkiro shi ne "Sayar da gandun ganyen shayi na Ti maimakon sayar da ganyen shayi", wato ana neman janyo hankalin mutanen wurare daban daban domin su sayi gandun ganyen shayi, daga baya za su iya sa ido kan yadda ake sarrafa ganyen shayin na Ti ta wayar salula. Ban da wannan kuma an gayyaci manoma masu shuka ganyen shayi na kauyuka 10 domin su yi hadin gwiwa da kamfanin, inda aka samar da wani cikakken tsari don tabbatar da ingancin ganyen shayin da aka samar.

A cewar Madam Xiang Zhonghong, wata jami'a a wurin, yanzu a dukkan gandayen ganyen shayi na wurin da fadin su ya kai fiye da muraba'in kilomita 2.5, an sanya na'urori sa ido kan yadda ake sarrafa ganyen shayi na Ti.

"Dukkan manoman za su iya shiga cikin wannan tsari, inda za su iya yin amfani da dandalin da muka kafa, don sayar da kayayyakinsu, tare da samun karin kudin shiga."

Zuwa yanzu, ganyen shayin da aka samar a wannan wuri yana samun karbuwa sosai a kasuwanni daban daban na kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China