Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa masu yaki da kwararar hamada
2020-09-04 16:51:43        cri

 




Taklimakan, hamada ce mafi girma a kasar Sin, wadda fadinta ya kai muraba'in kilomita dubu 330. Hamadar tana jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, kuma wata hanya mai tsawon kilomita sama da 560 ta ratsa hamadar, a yayin da a gefenan hanyar, aka dasa bishiyoyin da fadinsu ya kai kimanin mita 72 zuwa 78.

A karshen shekarun 1980, kasar Sin ta fara aikin binciken albarkatun man fetur a hamadar, sai dai matsalar ita ce babu hanya, da wuya a yi zirga-zirga a cikin hamadar, kuma da manyan motoci na musamman ne aka yi jigilar kayayyakin bincike da ma na rayuwa. Don haka, a shekarar 1993, an kaddamar da aikin gina hanyar da ta ratsa hamadar, kuma malam Xu Xinwen, manazarci a cibiyar nazarin harkokin muhalli da yanayin kasa ta jihar Xinjiang karkashin kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban cibiyar nazarin fasahar gyara hamada ta zama dausayi ta kasar, ya shiga aikin gina hanyar tun farko.

A shekarar 1995, an kammala gina hanyar, kuma bayan da aka kaddamar da ita, ta samar da saukin aikin binciken mai a hamadar, baya ga haka, ya kuma rage hanyar tsakanin birnin Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang, da birnin Hetian da kilomita 500, wanda ya taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin wurin.

Duk da cewa an cimma nasarar gina hanyar, kasancewarta a cikin hamada, in iska ta taso, za ta iya kwashe rairayi har sun mamaye hanyar baki daya, abin da ya kasance babbar matsala da ke gaban magina hanyar, wato ta yaya za a kare hanyar daga rairayi ta yadda za ta gudana yadda ya kamata. A game da wannan, malam Xu Xinwen ya ce, da aka gina hanyar, a kan kafa wasu shingaye da kara ko ciyayi don kare hanyar, sai dai matsalar shingayen ita ce ba za su dore ba. Don neman warware matsalar, sun yi kokarin nazarin dabarar dasa tsarin bishiyoyi na kare hanyar. Amma aikin ba shi da sauki, sabo da matsanancin yanayin da ake ciki a hamadar, ban da iska da rairayi, ga shi kuma babu ruwa mara gishiri a wurin. Gishirin da ke cikin ruwan wurin na cubic mita guda zai iya kai kilogiram 3 zuwa 30. Ya ce, "Da farkon fari, an kafa tsarin shingayen da aka kafa da ciyayi ne a tsawon gefunan hanyar da ta kai kilomita sama da 400, amma a sa'i daya, muna kuma gudanar da gwajin dasa bishiyoyi. Daga shekarar 1992, mun fara gwajin ne a iyakar hamadar, ya zuwa shekarar 1995, bayan da aka shimfida hanyar cikin zurfin hamadar, mu ma mun kaurar da wurin gwajin zuwa can. Mun yi ta gudanar da gwajin ba tare da tsayawa ba, wato zabar tsirran da suka dace mu dasa a cikin zurfin hamadar Taklimakan tare da ban musu ruwa mai gishiri, don mu gani wadanne suka iya tsira tare da ba da kariya ga hamadar. Ya zuwa shekarar 1997, mun san tsirran da suka dace, to, daga lokacin, muka fara gwajin kafa tsarin bishiyoyi a wani sashe na hanyar."

Kwalliya ta biya kudin sabulu, a shekarar 2003, a hukunce ne aka fara gina tsarin kariya na bishiyoyi a gefunan hanyar, kuma ya zuwa shekarar 2006, an kammala aikin. Tsarin kariya da aka gina yana da tsawon kilomita 436 da kuma fadin mita 72 zuwa 78, gaba daya kuma aka gina bishiyoyi sama da miliyan 20. Baya ga haka, an kuma gina rijiyoyi 108 a gefen hanyar. A cikin shekaru kimanin 15 da suka wuce, tsarin ya tabbatar da gudanar hanyar yadda ya kamata, baya ga haka, muhallin sassan da hanyar ta ratsa ma sun inganta sosai.

Labarin wannan tsarin kariya da aka gina da bishiyoyi cikin hamada ya jawo hankalin gida da kuma waje, ciki har da Libya, wadda ita ma ke fuskantar matsalar kwararowar hamada. Don haka, gwamnatin kasar ta wancan lokaci ta samu masanan cibiyar nazarin, don neman hadin gwiwa da su ta fannin kare kwararowar hamada. Malam Xu Xinwen ya ce,  "Na je ofishin ministan noman Libya, da kuma ma'aikatar kiyaye muhalli, don bayyana yadda muke gudanar da wannan aiki a hamada, wanda ya ba su sha'awa sosai. Ya zuwa shekara mai zuwa, darektan kwamitin yaki da kwararowar hamada na kasar ya kawo mana ziyara tare da wani masanin ban ruwa da kuma wani masanin ilmin tsirrai, bayan ziyararsu kuma, sun kara gayyatarmu zuwa kasarsu, don mu yi nazari a kan yanayin hamadar kasar."

A shekarar 2009, bisa goron gayyatar da tsohuwar gwamnatin kasar ta ba su, masanan cibiyar nazarin muhalli da yanayin kasa ta jihar Xinjiang sun tsara shirin daidaita matsalolin da ake fuskanta a hanyar da ta ratsa hamadar Murzuq, shirin da kwamitin yaki da kwararowar hamada na kasar ya karba.

Daga nan kuma, sai cibiyar ta yi hadin gwiwa da kasashen Mauritania da Nijeriya da Habasha da sauransu.

Umar Danladi Dahiru, wanda shi ne darektan cibiyar rajin kare kwararowar hamada a kasashen Afirka (Africa Desertification Control Initiative Nigeria) , cibiyar da aka kafa ta a shekarar 2008 da nufin wayar da kan al'umma da ba da shawarwari da kuma hadin gwiwa da kungiyoyi da kasashen da wadanda za su taimaka wajen shawo kan matsalar kwararowar hamada da kasashen Afirka ke fama da ita. A game da matsalar kwararowar hamada da Nijeriya ke fuskanta, ya kuma bayyana mana cewa, "Matsalar kwararowar hamada a Najeriya tana kawo abubuwa na damuwa kwarai da gaske, kwararowar jama'a daga kayuka zuwa birare, saboda yadda hamadar ta mamaye musu gonakin da suke noma da kiwo, shi ne kuma manyan sana'o'in mutanenmu a yankunan karkara. Don haka, idan wannan hamada ta zo ta mamaye musu gonaki, ba su da wani abin yi, sai dai su zo cikin birane. Idan kuma sun zo cikin birane, ba su wasu takamaiman abin yi, sai ki ga ana ta kame-kame ana ta abubuwa da sauransu. Shi ne muka ga ya kamata a tashi haikan domin a wayar da kan jama'a game da wannan abin tukuna. Mutane su ma sun ga cewa, ga irin muhallin da ke ciki. Saboda abubuwan da muke yi wadanda suke kara tunzura kwararowar hamadar nan, ya kamata a wayar da kan jama'a cewa, a dan rage su don a samu sa'ida. Sannan kuma a mayar da hankali wajen dasa bishiyoyi da sauransu, wanda kuma muna kan cimma manufar mu kan wannan yunkuri da muke yi."

Domin daidaita matsalar da suke fuskanta, yau kimanin shekaru 10 da suka wuce, sai suka fara kulla huldar hadin gwiwa da cibiyoyin nazari na kasar Sin, cibiyar nazarin harkokin muhalli da yanayin kasa ta jihar Xinjiang na daya cikinsu. Malam Umar ya ce, "Ita ma ta samar da kwasa-kwasai,wanda ya ke mun je mun halarta, kuma ta shirya tafiye-tafiye na gani da ido, wanda daga nan ta gayyace mu, har da jami'an gwamnati ta karkashin wannan kungiyar mu mai zaman kanta (NGO) muka je kasar Sin da su, ba sau daya ba. Su ka ga yadda ake amfani da fasahohi na kare kwararar hamada a wannan wuri. Tun da wannan yanki yana daya daga cikin masu fama da kwararar hamada. Suna kuma da hamadodi iri-iri a wannan bangare. Mun ziyarci wannan wuri, mun ga yadda abubuwa suke, da fasahar da aka yi amfani da ita wajen dakile kwararar hamada da irin abubuwan da aka yi da su wajen inganta rayuwar jama'a da suke zaune a irin wadannan wurare"

Malam Umar ya ce, tsarin kariya da shuke-shuke da aka gina a gefunan hanyar da ta ratsa hamadar Taklimakan ya burge shi matuka a yayin ziyarar da ya kai jihar Xinjiang, ya ce, "Ba ma ni ba, duk wanda ya je abubuwan da suka gani sun burge su, saboda yadda aka gudanar da abubuwa yadda ya kamata. Kamar lokacin da muka je hamadar Taklimakan, mu ga wannan shuka da aka yi kilomita 450, tsawon kamar daga nan zuwa Abuja, hagu da dama an kare, kuma Titi gashi nan lafiya lau, amma gyefe da gyefensa, hamada ce iya ganinka babu iyaka. Amma saboda shukan da aka yi,kilomita 450 da fadinta mita 15, ya janyo wannan titi ya tsira, motoci suna shiga har cikin wannan hamada, ana ma hakar man fetur a cikin wannan waje, wannan abu ya ba mu sha'awa kwarai da gaske, duk wanda ya je wannan waje, abin ya ba shi sha'awa, aiki ne jajurcacce da aka tsaya aka yi shi. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu."

Cistanche wani nau'in tsirrai ne da ya ke rayuwa cikin hamada, kana wani magani ne mai daraja. A cikin 'yan shekarun baya, cibiyar nazarin harkokin muhalli da yanayin kasa ta jihar Xinjiang ta dukufa wajen noman tsirran a cikin hamada, ta yadda za a rika samun kudi daga aikin kiyaye muhalli, ta yadda aikin kare muhalli zai dore. Masanan cibiyar sun kuma kai wannan dabarar Nijeriya.

Malam Wang Yongdong, mataimakin manazarci ne a cibiyar nazarin harkokin muhalli da yanayin kasa ta jihar Xinjiang, ya taba kai ziyara sau biyu jihar Kano ta Nijeriya, don gudanar da bincike tare da yin musayar ra'ayoyi tare da takwarorinsu na Nijeriya. Ya ce, kwararowar hamada ta kan haifar da matsalar talauci, don haka, su kan mai da hankali a kan inganta rayuwar mazauna wurin a yayin da suke kyautata muhallinsu.

Ya ce, "Manufar da muke bi ita ce a hada aikin kiyaye muhalli da inganta rayuwar al'umma. Don haka, a Nijeriya muka ba da shawarar a kara dasa bishiyoyin da za su iya samar da arziki, sabo da baya ga kare iska da rairayi, bishiyoyin za su taimaka ga bunkasa tattalin arzikin wurin. A lokacin, suna da nau'in bishiya da ake kira bishiyar karo, wanda kuma ake daukarsa a matsayin zinari na hamada, don haka, mun ba su shawarar habaka su. "

A gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da ya gudana a shekarar 2018 a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana muhimman matakan da za a dauka daga wasu fannoni takwas, ciki har da hadin gwiwar sassan biyu ta fannin kiyaye muhalli.  Malam Wang Yongdong ya ce, yanzu suna gudanar da wani shiri na kafa wata cibiyar samar da misali a Nijeriya. Ya ce, "Muna fatan gabatar da ingantattun fasahohinmu da kuma dabaru, bisa kuma yin la'akari da yanayin da ake ciki a kasar, don samar da wani tsarin da zai kara kudin shigar mazauna wurin tare kuma da kare muhallinsu."

Malam Xu Xinwen ya shafe tsawon shekaru sama da 30 yana aiki da takwarorinsa na kasar Sin masu aikin yaki da kwararar hamada, inda suka rika kyautata muhallin hamada. Ya ce, kwararar hamada kalubale ne da ke gaban baki dayan bil- Adam, don haka yake fatan karin kasashe za su amfana da fasahohin kasar Sin. Ya ce, "Mun shafe gomman shekaru muna ta kokari a wannan fanni, kuma mun karu da fasahohi da ma dabarun da za mu iya yayata wa, fatanmu shi ne za mu iya raba su ga kasashen Afirka, da ma kasashen yammacin da tsakiyar nahiyar Asiya, don mu kara ba da gudummawa wajen shawo kan matsalar kwararowar hamada."

A jawabin da ya gabatar a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da ya gudana a shekarar 2018 a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, "Duniyar bil Adam baki daya ce, kasar Sin na son hada kai da Afirka, don a rika yayata hanyoyin samun ci gaba mai dorewa ba tare da gurtaba muhalli ba, ta yadda za mu kare muhallinmu da kuma halittun duniyar. Haka kuma Kasar Sin tana son hada kai da Afirka wajen tinkarar sauyin yanayi da yin amfani da makamashi mai tsabta da kuma shawo kan kwararowar hamada da kiyaye namun daji da sauran halittu, ta yadda sassan biyu za su iya tabbatar da jituwa a tsakanin al'ummunsu da kuma halittu." 

Yanzu kiyaye muhalli ya kasance wani muhimmin bangare na hadin gwiwar Sin da Afirka, wanda ke da kyakkyawar makoma, wanda kuma zai dinga inganta hadin gwiwar sassan biyu.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China