Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren hukumar lafiyar Amurka: Watsi da batun annoba don share fagen cimma muradun siyasa
2020-08-11 12:20:57        cri
Da yammacin ranar 9 ga wata, sakataren hukumar lafiya da hidimar al'umma ta kasar Amurka Alex Azar, ya isa birnin Taipei, kamar yadda kafar yada labaran yankin Taiwan ta bada rahoto.

A game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a taron manema labarai da ya gudana jiya cewa, kasar Sin tana Allah wadai da musayar dake gudana tsakanin jami'an kasar Amurka da na yankin Taiwan.

Azar ya ziyarci yankin Taiwan, inda ya fake da batun hadin gwiwar yaki da annoba, tare da boye hakikanin manufar ziyararsa. Abin mamakin shi ne, ya zuwa ranar 9 ga wata, mutane sama da miliyan 5.05 ne aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, kana mutane sama da 160,000 cutar ta kashe a Amurka, kamar yadda alkaluman jami'ar Johns Hopkins ta fitar.

Mr. Azar yana baiwa bangaren siyasa fifiko sama matsalar annobar da ta yi kamari a kasar, kamar yadda wani jami'in tsohuwar gwamnatin Obama ya bayyana. Wani shafin yada labaran siyasa na Amurka na yanar gizo mai suna "Politico", ya wallafa cewa yawan ziyarce-ziyarce da Azar ke kaiwa jihohin da shugaba Trump ke fuskantar rashin tabbas a babban zaben da za a gudanar da kuma yadda yake cigaba da nuna kauna kan shugaba Trump ya bada mamaki ga jami'an gwamnatin mai ci da na gwamnatin da ta shude a hukumar lafiyar kasar, a daidai lokacin da annobar ke kara kamari wadda ke matukar bukatar daukar cikakkun matakan kawar da ita.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China