Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Batun intanet mai tsafta na Amurka ya raba kan tsarin Intanet na duniya
2020-08-11 11:47:50        cri

A kwanakin baya ne, shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya sanya hannu kan dokar shugaba, inda ya haramta duk wani Ba-Amurka ko wani kamfanin kasar, yin huldar kasuwanci da manhajar Wechat da kamfanin Tencent na kasar Sin cikin kwanaki 45.

Sai dai kafar watsa labarai ta Bloomberg ta yi imanin cewa, kasar Sin ta kasance kasuwa mai muhimmanci ga kamfanin Apple, a saboda haka, haramcin da Trump ya sanyawa Wechat, na iya yin babban tasiri kan Apple a kasuwannin kasar Sin. Idan kuma haramci ya ci gaba, a hannu guda kuma Apple ya gaza daidaita lamarin, mai yiwuwa masu sayayya a kasar Sin su koma yin amfani da Huawei, wayar salula ta zamani da ake sarrafawa a kasar Sin. Idan kuma har haka ta faru, kamfanonin kasar Sin ne za su ci riba.

A cewar kafar watsa labarai ta BBC, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya sanar da cewa, kasar Amurka za ta kaddamar da abin da ya kira, "tsarin Intanet mai tsafta" domin fitar da kamfanonin kasar Sin daga tsarin Intanet na Amurka. Sai dai masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na cewa, tsarin intanet mai tsafta da Amurkar ke son fito da shi, zai kara takaita harkokin Intanet na duniya, maimakon tsarin Intanet da ya karade duniya da babu rufa-rufa a cikinsa.( Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China