Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin 'yan siyasar Amurka na dorawa wasu laifi ba zai yi nasara ba
2020-08-06 19:59:34        cri

A ranar 4 ga wata, babban editan mujallar The Lancet Richard Horton ya wallafa wani rahoto a jaridar The Guardian ta Birtaniya, inda ya yi nuni da cewa, 'yan siyasar kasashen yamma suna shafawa kasar Sin kashin kaji karkashin jagorancin gwamnatin kasar Amurka, domin dora laifin yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ga kasar Sin, amma hakika masana kimiyyar kasar Sin suna taka babbar rawa yayin da ake kokarin dakile annobar a fadin duniya.

Rahoton Horton ya nuna hakikanin abu wato kusan daukacin al'ummun kasashen duniya sun gano yunkurin 'yan siyasar Amurka na neman dora laifi, kana an lura cewa, 'yan siyasar Amurka sun kasa daukan sabbin matakai, maimakon haka, sai ci gaba da dora laifi ga kasar Sin, inda suka sha ambaton "kwayar cutar kasar Sin" a wurare daban daban, har kafofin watsa labaran Amurka su ka ji kunya. A kwanakin baya mai ba da shawara kan harkokin cinikayya na fadar White House Peter Navarro ya yi hira da menama labaran CNN, inda ya sake bayyana kalaman "kwayar cutar kasar Sin", inda nan take jagoran shirin ya katse masa hanzari, kuma ya bayyana cewa, "Kada ka ci gaba da fadan wannan kalma a cikin shirina".

A halin yanzu, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a jihohi daban daban na Amurka ya karu sakamakon gaza hana yaduwarta da matakan farfadowar tattalin arzikin da aka dauka, a sa'i daya kuma, adadin GDP na kasar a rubu'i na biyu ya ragu da kaso 32.9 cikin dari, duk wadannan sun jefa al'ummun kasar ta Amurka cikin mawuyacin hali, kana alkaluman bincike sun nuna cewa, goyon bayan da al'ummun kasar suke nunawa shugaban kasar kan aikin dakile annobar COVID-19 ya ragu zuwa kaso 34 cikin dari.

Ban da haka, masu tsattsauran ra'ayi kalilan a Amurka suna baza jita-jita iri daban daban domin shafawa kasar Sin kashin kaji saboda kyamarsu kan kasar Sin, wannan makarkashiyar salo ne na tayar da wani yakin cacar baki ga kasar Sin.

Yanzu an riga an shiga karni na 21, idan har aka tayar da yakin cacar baki, hakika, zai kawo cikas ga ci gaban tarihi, sheihun malamin jami'ar Harvard Ezra Feivel Vogel ya taba bayyana cewa, mayar da kasar Sin abokiyar gaba, bai dace da moriyar kasar Amurka ba, a don haka duk da cewa, 'yan siyasar Amurka suna zargin kasar Sin kamar yadda suke so, amma an riga an gano mawuyacin yanayin da suke ciki sakamakon gaza warware matsalolin da suke fuskata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China