Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana sa ran duniya za ta iya cin gajiyar hidimar BeiDou a bangaren sanin inda ake na kimanin matsayin sentimita
2020-08-04 12:49:17        cri

Kasar Sin ta sanar da kammalawa da ma kaddamar da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na kasa da kasa na BeiDou-3 a hukumance a ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata. Darektan ofishin kula da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 na kasar Sin kana kakakin tsarin na BeiDou Ran Chengqi, shi ne ya sanar da haka Litinin din nan, yayin taron manema labarai da aka shirya. Yana mai cewa an fitar da kayayyakin da suka shafi tsarin zuwa sama da kasashe da yankuna 120, inda yake samar da hidima ga sama da mutane miliyan 100.

Tsarin shawagin tauraron dan-Adam na kasa da kasa na BeiDou-3 na daya daga cikin tsarukan shawagin tauraron dan Adam na kasa da kasa guda 4 da suka samu amincewa daga wajen MDD. A kwanan baya, Mr. Ran Chengqi, Darektan ofishin kula da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 na kasar Sin kana kakakin tsarin na BeiDou ya bayyana cewa, a lokacin da aka kafa tsarin shawagin tauraron dan-Adam na kasa da kasa na BeiDou, a kullum kasar Sin tana fatan zai iya ba da hidimomi masu inganci ga duk wanda zai yi amfani da shi a duk fadin duniya.

"Yanzu ana kokarin zurfafa hadin gwiwa da kuma yin cudanya tsakanin tsarin Beidou da na GPS na Amurka da na GLONASS na Rasha da na GNSS na EU. Sannan an shigar da tsarin COMPASS na Beidou na kasar Sin kungiyar zirga-zirgar jiragen saman jama'a ta ICAO da ta harkokin teku ta kasa da kasa ta IMO da kungiyar kula da aikin ceto ta taurarin dan Adam ta COSPAS/SARSAT da kungiyar wayar salula ta Inmarsat da dai makamatansu. Bugu da kari, an fitar da wasu ma'aunonin kasa da kasa da suke goyon bayan tsarin COMPASS na Beidou. A kasar Tunisiya, an kafa cibiyar kula da tsarin Beidou, sannan an samu kwangilar gina tsarin karfafa alamun tsarin shawagin tauraron dan-Adam na kasa da kasa na BeiDou. A yayin taron ministoci karo na 9 na dandalin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa, bangarorin biyu sun tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa a bangaren tsarin Beidou. Kawo yanzu, an fitar da kayayyakin da suka shafi tsarin zuwa sama da kasashe da yankuna 120, inda yake samar da hidima ga sama da mutane miliyan 100. Yankunan ASEAN da Kudancin Asiya da Gabashin Turai da Yammacin Asiya da Afirka, suna amfani da tsarin na BeiDou a fannonin tsara taswira da aikin gona da gine-gine da tashoshin ruwa na zamani."

Ran Chengqi ya bayyana cewa, idan an kwatanta tsarin Beidou da makamancin tsarukan shawagin tauraron dan-Adam na kasa da kasa, tsarin Beidou yana da halayyarsa ta musamman a fannoni biyu. Da farko dai, zai iya samar da gajeren sako, wato za a iya aikewa da garejen sako bisa amfani da tsarin, idan babu goyon bayan tsarin sadarwa na tafi da gidanka a doron duniya. Sannan tsarin Beidou zai iya ba da hidima mai inganci matuka.

Ran Chengqi ya kara da cewa, a nan gaba tsarin na BeiDou zai rika samar da hidimomi masu inganci a duniya, da gina tsarin sanin inda ake da shawagi a fannin lokaci. Mr. Ran yana mai cewa, "Nan gaba ba da dadewa ba, za mu gina wani tsarin taurarin dan Adam a sararin samaniya da bai yi nesa da doron duniyarmu ba. Sakamakon haka, ana yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2025, duniya za ta iya cin gajiyar hidimar BeiDou a bangaren sanin inda ake na kimanin matsayin sentimita."

Bugu da kari, Mr. Ran Zongqi, Darektan ofishin kula da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 na kasar Sin kana kakakin tsarin na BeiDou, ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan kudin da aka samu daga hidimomi da masana'antun da suke shafar tsarin shawagin tauraron dan-Adam da tsarin sanin inda ake da shawagi a fannin lokaci ya karu fiye da kashi 20 cikin dari a kowace shekara, wato ya kai RMB yuan biliyan 345 a shekarar 2019. An yi hasashen cewa, wannan adadi zai kai RMB yuan biliyan 400. Yanzu tsarin shawagin tauraron dan Adam na Beidou yana ba da hidimomi ga sana'o'in sufurin kayayyaki, da tsaron jama'a, da aikin rigakafi da fama da bala'u daga indallahi, da ayyukan gona da kiyaye gandun daji da kiwon dabbobi da kayayyakin ruwa da kuma aikin tafiyar da harkokin yau da kullum a birane, har ma yana taka muhimmiyar rawa a bangarorin wutar lantarki da hada-hadar kudi da sadarwa da dai sauran muhimman kayayyakin yau da kullum na kasar Sin. Mr. Ran Chengqi ya bayyana cewa, kawo yanzu, an samu nasarar samar da dukkan kananan na'urorin da suke da nasaba da tsarin Beidou ga na'urorin wayar salula. Mr. Ran yana mai cewa, "Yanzu ana iya shigar da hidimomin tsarin Beidou cikin yawancin na'urorin wayar salula ta tafi da gidanka." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China