Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai rashin tabbas game da kasancewar Wuhan cibiyar bullar cutar COVID-19 ta farko in ji wani kwararre
2020-08-04 11:09:04        cri

Babban daraktan sashen ayyukan gaggawa na hukumar lafiya ta duniya WHO Dr. Michael Ryan, ya ce duk da cewa a birnin Wuhan na kasar Sin aka fara samun adadi mai yawa na al'ummun da suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19, hakan ba ya tabbatar da cewa, birnin ne wurin da wata dabba ta fara yada cutar zuwa bil Adama a duniya.

Dr. Michael Ryan, wanda ya bayyana hakan yayin da yake bayyana halin da ake ciki game da cutar ta COVID-19 da safiyar jiya Litinin, ya jaddada muhimmancin zurfafa bincike, game da wuraren da aka samu dandazon mutane da suka harbu da cutar a karon farko, da yanayin bazuwar ta, don gano hakikanin abun da ya auku tun farkon bullar annobar.

Dr. Ryan ya ce a baya bayan nan, kwararrun hukumar ta WHO da suka ziyarci kasar Sin, don gudanar da aikin bankado tushen cutar sun kammala aikin su, yayin da ake sa ran binciken da zai biyo baya, zai kara haska ma'anar wanda masanan kasar Sin suka gudanar a kasuwar sayar da naman ruwa ta birnin Wuhan, inda a baya aka samu barkewar annobar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China